Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb22 Maris p. 5
  • Hanyoyi Uku da Za Mu Dogara ga Jehobah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Hanyoyi Uku da Za Mu Dogara ga Jehobah
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
  • Makamantan Littattafai
  • Gatan da Muke da Shi Na Yin Addu’a
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Ka Rika Yin Addu’a don Ka Kusaci Allah
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Yaya Kake Tsai da Shawarwari?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Ka Tsai Da Shawarwari Da Ke Ɗaukaka Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
mwb22 Maris p. 5

RAYUWAR KIRISTA

Hanyoyi Uku da Za Mu Dogara ga Jehobah

Dauda ya yi nasara a kan Goliyat don ya dogara ga Jehobah. (1Sam 17:45) Jehobah yana so ya taimaka wa bayinsa. (2Tar 16:9) Ta yaya za mu dogara ga Jehobah maimakon mu dogara ga kanmu? Ga hanyoyi uku:

  • Ku riƙa addu’a a kai a kai. Bai kamata mu riƙa addu’a kawai don neman gafarar zunubanmu ba, amma don mu sami ƙarfin jimre jarrabawa. (Mt 6:12, 13) Mu riƙa addu’a don neman ja-gorancin Jehobah da hikimarsa kafin mu yanke shawarwari. Bai kamata mu riƙa neman albarkarsa kawai bayan mun yanke shawara ba.—Yak 1:5

  • Ku tsara yadda za ku riƙa karanta Littafi Mai Tsarki da kuma nazarinsa. Ku dinga karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana. (Za 1:2) Ku riƙa tunani game da misalan bayin Allah da aka ambata a Littafi Mai Tsarki, kuma ku yi amfani da darussan da kuka koya. (Yak 1:23-25) Ku riƙa shiri don wa’azi maimakon ku riƙa amfani da abin da kuka sani a dā kawai. Ku riƙa shirya abubuwan da za a yi nazarinsu a taro don ku amfana sosai

  • Ku riƙa yin abin da ƙungiyar Jehobah ta gaya muku. Ku yi ƙoƙari ku san kuma ku bi umurnan da ƙungiyar Jehobah take bayarwa kwanan nan. (L.Ƙi 9:17) Ku bi umurnan da dattawa suke ba ku.—Ibr 13:17

’Yan sanda sun kama wani dan’uwa, kuma masu wasa labarai da wasu ’yan’uwa suna wurin.

KU KALLI BIDIYON NAN KADA KU JI TSORON TSANANTAWA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

• Mene ne ya sa ’yan’uwan tsoro?

• Me ya taimaka musu su daina jin tsoro?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba