Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb22 Janairu p. 11
  • Matasa, Ku Rika Gaya wa Iyayenku Abin da Ke Damunku

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Matasa, Ku Rika Gaya wa Iyayenku Abin da Ke Damunku
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
  • Makamantan Littattafai
  • “Ka Girmama Mahaifinka da Mahaifiyarka”
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
  • Za Ku Iya Sa Iyalinku Su Daɗa Farin Ciki
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Iyaye, Ku Koya wa Yaranku Su Ƙaunaci Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Ku Yi Amfani da Ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki Ku Taimaka Wa Yaranku
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
mwb22 Janairu p. 11

RAYUWAR KIRISTA

Matasa, Ku Riƙa Gaya wa Iyayenku Abin da Ke Damunku

Me ya sa zai dace ku riƙa gaya wa iyayenku abin da ke zuciyarku? (K. Ma 23:26) Domin Jehobah ya ba su hakin kula da ku da kuma taimaka muku. (Za 127:3, 4) Zai yi musu wuya su taimaka muku idan kuka ɓoye abin da ke damunku. Kuma ba za ku san abubuwa game da rayuwa da suka sani ba. Laifi ne ku bar wasu abubuwa a zuciyarku? Ba lallai ba, muddin ba ku ruɗi iyayenku ba.—K. Ma 3:32.

Ta yaya za ku yi magana da iyayenku? Ku zaɓi lokacin da ya dace. Idan hakan zai yi wuya, za ku iya rubuta wa mamarku ko babanku wasiƙa don ku bayyana yadda kuke ji. Idan kuma iyayenku suna so su tattauna wani batu da ba za ku so ku tattauna da su ba fa? Ku tuna cewa suna so su taimaka muku ne. Iyayenku abokanku ne ba maƙiyanku ba. Idan kun yi ƙoƙarin tattaunawa da iyayenku, za ku amfana har abada!—K. Ma 4:10-12.

KU KALLI BIDIYON NAN RAYUWAR MATASA—TA YAYA ZAN YI WA IYAYENA MAGANA? SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Hoton da aka dauko daga bidiyon “Rayuwar Matasa—Ta Yaya Zan Yi wa Iyayena Magana?” Wata yarinya da ta saka headphone kuma tana amfani da kwamfuta, ta ki saurarar mahafiyarta da ke yi mata magana.

    Mene ne Esther da Partik suka fahimta game da kansu?

  • Hoton da aka dauko daga bidiyon “Rayuwar Matasa—Ta Yaya Zan Yi wa Iyayena Magana?” Wata yarinya tana magana da mahaifiyarta kuma tana nuna mata wani abu a wayarta.

    Mene ne za ka iya koya daga misalin Yesu?

  • Hoton da aka dauko daga bidiyon “Rayuwar Matasa—Ta Yaya Zan Yi wa Iyayena Magana?” Wata mahaifiya ta dan bar yin aikace-aikacen gida kuma tana wasa da danta.

    Ta yaya iyayenka suka nuna maka cewa sun damu da kai?

  • Hoton da aka dauko daga bidiyon “Rayuwar Matasa—Ta Yaya Zan Yi wa Iyayena Magana?” Wani kocin kwallon kwando ya zana wa ’yan wasansa yadda za su yi wasa a kan allo.

    Iyayenka suna so ka yi nasara

    Waɗanne ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ne za su taimaka maka ka iya yi wa iyayenka magana?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba