Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb21 Nuwamba p. 9
  • Ta Yaya ’Yan’uwa Mata Za Su Biɗi Ƙarin Aiki?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ta Yaya ’Yan’uwa Mata Za Su Biɗi Ƙarin Aiki?
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Rika Karfafa ʼYan’uwa Mata
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Kana Daraja Mata Yadda Jehobah Yake Yi?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Me Ya Sa Kiristoci Suke Bukatar Su Ƙara Ƙoƙari a Hidimarsu?
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
  • Yadda Za Mu Fahimci Shugabanci a Ikilisiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
mwb21 Nuwamba p. 9
Hotuna: ’Yan’uwa mata suna ayyuka dabam-dabam da farin ciki. 1. Wata ’yar’uwa tana wa’azi. 2. Wata ’yan’uwa tana aikin gine-gine. 3. Wata ’yar’uwa tana share Majami’ar Mulki. 4. Wata ’yar’uwa tana nuna wa wata tsohuwa yadda ake amfani da waya. 5. Wata ’yar’uwa tana taimaka wa ’yarta ta yi kalami a taro. 6. ’Yan’uwa mata biyu suna wa’azi sa’ad da ake sanyi.

RAYUWAR KIRISTA

Ta Yaya ’Yan’uwa Mata Za Su Biɗi Ƙarin Aiki?

’Yan’uwa mata suna taimakawa sosai a ayyukan da suka shafin wa’azi game da Mulkin Allah. (Za 68:11) Suna nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane da yawa. Su suka fi yawa a cikin masu hidimar majagaba na kullum. ’Yan’uwa mata da yawa suna hidima a Bethel, da wa’azi a ƙasashen waje, da aikin gine-gine na gida da na ƙasashen waje, da kuma fassara. ’Yan’uwa mata da suka manyanta suna ƙarfafa iyalinsu da kuma ikilisiya. (K. Ma 14:1) Ko da yake ’yan’uwa mata ba za su iya zama dattawa ko bayi masu hidima ba, za su iya kafa maƙasudai. A waɗanne hanyoyi ne ’yar’uwa mata za su iya biɗan ƙarin aiki?

  • Ku riƙa nuna halayen masu kyau da za su ƙarfafa dangantakarku da Jehobah.​—1Ti 3:11; 1Bi 3:3-6

  • Ku taimaka wa ’yan’uwa mata da ba su manyanta ba tukuna.​—Tit 2:3-5

  • Ku riƙa yin wa’azi sosai kuma ku inganta yadda kuke yin wa’azi

  • Ku koyi wani yare

  • Ku je hidima a wuraren da ake bukatar masu shela

  • Ku cika fom na yin hidima a Bethel ko kuma taimaka da gina wuraren ibada

  • Ku cika fom na Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki

KU KALLI BIDIYON NAN ‘MATA MASU HIDIMAR UBANGIJI DA ƘWAZO,’ SAI KU AMSA TAMBAYA NA GABA:

  • Ta yaya kalaman ’yan’uwa matan nan suka ƙarfafa ka?

’Yan’uwa mata uku da suka fito a bidiyon “Mata Masu Hidimar Ubangiji da Kwazo.”
    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba