Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb21 Satumba p. 5
  • Kuna Horar da Kanku don Ku Yi Abin da Ya Dace

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kuna Horar da Kanku don Ku Yi Abin da Ya Dace
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Za Ka Tsai da Shawarwari Masu Kyau
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ka Kasance da Bangaskiya Kuma Ka Tsai da Shawara Mai Kyau!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Ka Tsai Da Shawarwari Da Ke Ɗaukaka Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Gabatarwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2024
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
mwb21 Satumba p. 5

RAYUWAR KIRISTA

Kuna Horar da Kanku don Ku Yi Abin da Ya Dace

Wajibi ne ɗan wasa ya ci gaba da horar da kansa don ya ƙware. Hakazalika, dole mu ci gaba da ƙoƙari don mu horar da kanmu kuma mu yi abin da ya dace. (Ibr 5:14) Ko da za mu iya ganin cewa ya fi sauƙi mu bi shawarwarin da wasu suka yanke, wajibi ne mu koyi yadda za mu riƙa tsai da shawara da kanmu. Me ya sa? Domin kowannenmu ne zai ba da lissafi don shawarwarin da ya yanke.​—Ro 14:12.

Bai kamata mu riƙa ganin cewa za mu yanke shawarwari masu kyau don mun daɗe da yin baftisma ba. Don mu tsai da shawara mai kyau, muna bukatar mu dogara ga Jehobah da Kalmarsa da kuma ƙungiyarsa.​—Yos 1:​7, 8; K. Ma 3:​5, 6; Mt 24:45.

KU KALLI BIDIYON NAN “KU KASANCE DA LAMIRI MAI KYAU,” SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Hoto daga bidiyon “Ku Kasance Da Lamiri Mai Kyau.” Emma da mijinta suna kallon takardar gayyatar aure.

    Me ne ya ɗaure wa Emma kai?

  • Hoto daga bidiyon “Ku Kasance Da Lamiri Mai Kyau.” Amy tana bayana ra’ayinta.

    Me ya sa za mu guji gaya wa mutane abin da za su yi a batutuwan da ya kamata su yanke shawara da kansu?

  • Hoto daga bidiyon “Ku Kasance Da Lamiri Mai Kyau.” Emma ta nemi shawara daga wurin Charlotte da Allan.

    Wace shawara mai kyau ne wata mata da miji suka ba wa Emma?

  • Hoto daga bidiyon “Ku Kasance Da Lamiri Mai Kyau.” Emma tana yin bincike a “Watchtower LABURARE NA INTANE” a kwamfutarta.

    A ina ne Emma ta samu bayanin da ya taimaka mata?

Mene ne zai taimaka mini sa’ad da nake so in yanke shawara?

  • Ra’ayina

  • Ra’ayin wasu

  • Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba