Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb21 Yuli p. 3
  • Kauna da Tausayi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kauna da Tausayi
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Makamantan Littattafai
  • Allah Mai Tausayi Ne Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2018
  • Yin Tambayoyi
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Ka Ratsa Zukatan Mutane
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Yin Amfani da Kalmar Allah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
mwb21 Yuli p. 3

KA YI WA’AZI DA KWAZO | YADDA ZA KA DAƊA JIN DAƊIN WA’AZI

Ƙauna da Tausayi

Furucin nan ƙauna da tausayi yana nufin fahimtar ra’ayin mutane da yadda suke ji da daraja su da kuma sanin bukatunsu. Mutane sukan san lokacin da muke jin tausayinsu. Idan muna da ra’ayin taimaka wa mutane, za mu tausaya musu. Nuna ƙauna da jin tausayin mutane sa’ad da muke wa’azi ya dace. Domin hakan yana nuna cewa muna yin koyi da halin Jehobah na ƙaunar mutane da kula da su. Kuma zai sa mutane su kusace shi.​—Fib 2:4.

Ba a lokacin da muke koyarwa kawai muke nuna ƙauna da tausayi ba. Amma za mu nuna hakan ta saurarar mutane da kyau, ta furucinmu da halinmu da yadda muke motsa hannayenmu da kuma nuna fara’a. Muna nuna halin nan kuma ta wajen kula da mutane, da yin la’akari da abubuwan da suke so, da abin da suka yi imani da shi, da kuma yanayinsu. Ko da yake muna gaya musu abin da zai taimaka musu, ba za mu tilasta musu su canja ra’ayinsu ba. Za mu yi farin ciki sosai idan mutanen suka soma bauta wa Jehobah.

KU KALLI BIDIYON NAN ZA KU JI DAƊIN ALMAJIRTARWA IDAN KUN INGANTA YADDA KUKE WA’AZI​—KU NUNA ƘAUNA DA TAUSAYI, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Wani sashe na bidiyon ‘Za Ku Ji Dadin Almajirtarwa Idan Kun Inganta Yadda Kuke Wa’azi​—Ku Nuna Kauna da Tausayi.’ A wani kantin shayi, Rose ta bayyana dalilin da ya sa ba za ta iya yin nazari a ranar ba.

    Ta yaya Anita ta nuna ƙauna da tausayi a lokacin da Rose ta makara zuwa wurin da suka shirya yin nazari?

  • Wani sashe na bidiyon ‘Za Ku Ji Dadin Almajirtarwa Idan Kun Inganta Yadda Kuke Wa’azi​—Ku Nuna Kauna da Tausayi.’ Anita ta tausaya mata yayin da take sauraron ta.

    Ta yaya Anita ta nuna ƙauna da tausayi sa’ad da Rose ta ce ta gāji?

  • Wani sashe na bidiyon ‘Za Ku Ji Dadin Almajirtarwa Idan Kun Inganta Yadda Kuke Wa’azi​—Ku Nuna Kauna da Tausayi.’ Anita ta taya Rose shirya dakinta da ke birkici.

    Mutane za su so su koya game da Jehobah sa’ad da muka nuna musu ƙauna da tausayi

    Ta yaya Anita ta nuna ƙauna da tausayi sa’ad da Rose ta ce ita ba mai shirya kayayyaki ba ce?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba