Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb21 Janairu p. 9
  • Mun Gode wa Allah da Yesu don ’Yanci da Za Mu Samu a Nan Gaba

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mun Gode wa Allah da Yesu don ’Yanci da Za Mu Samu a Nan Gaba
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Makamantan Littattafai
  • Jehobah Yana Taimaka Mana Saꞌad da Muke Cikin Matsala
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Mu Rika Farin Ciki Sa’ad da Muke Jimre Jarrabawa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Ka Yi Godiya ga Jehobah Kuma Ka Sami Albarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
mwb21 Janairu p. 9
Yesu a kan kujerar sarauta yana kallon kasa ga hasken daukakar Jehobah a bayansa.

RAYUWAR KIRISTA

Mun Gode wa Allah da Yesu don ’Yanci da Za Mu Samu a Nan Gaba

Waɗanne matsaloli ne kake fuskanta a kowace rana? Kai magidanci ne da ke ƙoƙarin kula da iyalinka? Kai kaɗai ne ko ke kaɗai ce kike kula da iyalinki? Shin kana fuskantar cin zali daga tsararka a makaranta? Kana fama da rashin lafiya ne ko tsufa? Kowannenmu yana da matsala da yake fama da ita. Wasu ’yan’uwa ma suna fama da matsaloli da yawa a lokaci ɗaya. Duk da haka mun san cewa wata rana, Jehobah zai kawar da duka matsalolin.​—2Ko 4:​16-18.

Kafin lokacin, sanin cewa Jehobah ya fahimci matsalolin da muke fama da su na ƙarfafa mu sosai. Ban da haka ma, yana ɗaukan amincinmu da haƙurinmu da muhimmanci, shi ya sa ya yi alkawari cewa zai albarkace mu a nan gaba. (Irm 29:​11, 12) Yesu ma ya damu da mu. Yayin da muke ci gaba da ayyukan ibada, mu tuna da abin da Yesu ya gaya mana cewa: “Ina tare da ku.” (Mt 28:20) Idan mun dakata kuma muka yi bimbini a kan ’yancin da za mu samu a Mulkin Allah, hakan zai ƙarfafa begenmu kuma ya sa mu jimre matsalolin da muke fama da su.​—Ro 8:​19-21.

KU KALLI BIDIYON NAN KU ZUBA IDO GA YESU YAYIN DA BABBAN HADARI YAKE GABATOWA!​—ALBARKAR DA MULKIN ZA TA KAWO, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Mene ne ya ware ’yan Adam daga Allah, kuma mene ne sakamakon?

  • Waɗanne albarku ne bayin Allah masu aminci za su samu a nan gaba?

  • Me zai sa mu more waɗannan albarkun?

  • Me kake ɗokin ganin cikarsa a sabuwar duniya?

Hotunan mutane suna jin dadi a aljanna: Na 1. Wata mata ta rungumi wata da aka tayar daga mutuwa. Na 2. Suna jin dadin abinci da duniya mai tsabta da kuma salama da ke tsakaninsu.

Ka ga kanka a sabuwar duniya

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba