DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | FITOWA 35-36
An Shirya Su don Su Yi Aikin Jehobah
35:25, 26, 30-35; 36:1, 2
Ruhun Jehobah ya taimaka wa Bezalel da Oholiyab su gina mazauni kamar yadda aka tsara. (Ka duba hoton da ke shafin farko.) Jehobah yana ba bayinsa ruhu mai tsarki a zamaninmu. Ta yaya za mu amfana daga ruhu mai tsarki?
Dole ne mu roƙi Jehobah ya ba mu ruhu mai tsarki don mu kyautata yadda muke ayyuka a ƙungiyar Jehobah
Dole ne mu riƙa nazarin Kalmar Allah
Dole ne mu yi iya ƙoƙarinmu a duk wani aiki da aka ba mu
Waɗanne irin ayyuka ne Jehobah zai taimaka maka ka yi su?