24-30 ga Agusta
FITOWA 19-20
Waƙa ta 88 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 1)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Darussan da Muka Koya Daga Dokoki Goma”: (minti 10)
Fit 20:3-7—Ku girmama Jehobah kuma ku bauta masa shi kaɗai (mwbr20.08-HA an ɗauko daga w89 11/15 6 sakin layi na 1)
Fit 20:8-11—Ku saka bautar Jehobah farko a rayuwarku
Fit 20:12-17—Ku girmama mutane kuma ku yi musu biyayya (mwbr20.08-HA an ɗauko daga w89 11/15 6 sakin layi na 2-3)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 10)
Fit 19:5, 6—Me ya sa Isra’ila ta dā ba ta “zama mulki na firistoci” ba? (mwbr20.08-HA an ɗauko daga it-2 687 sakin layi na 1-2)
Fit 20:4, 5—Ta yaya Jehobah yake “hukunta ’ya’ya saboda zunuban iyayensu”? (w04 7/1 27 sakin layi na 1)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu game da Jehobah da wa’azi da dai sauransu?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Fit 19:1-19 (th darasi na 10)
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Haɗuwa ta Fari: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka soma da bin bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. Ka ba mutumin katin jw.org. (th darasi na 1)
Komawa Ziyara: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Ka soma da bin bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. Ka ba mutumin ɗaya daga cikin littattafanmu na wa’azi. (th darasi na 15)
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 5 ko ƙasa da hakan) bhs 68 sakin layi na 17-19 (th darasi na 8)
RAYUWAR KIRISTA
Ta Yaya Zan Sami ’Yancin Kaina?: (minti 6) Tattaunawa. Ku kalli wannan bidiyon zanen allo. Sai a yi wa matasa waɗannan tambayoyin: Ta yaya za ku sa iyayenku su amince da ku? Me ya kamata ku yi idan kuka yi kuskure? Ta yaya yin biyayya ga iyayenku zai sa ku sami ƙarin ’yanci?
Ku Daraja Iyayenku da Suka Tsufa: (minti 9) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon. Sa’an nan ku amsa waɗannan tambayoyin: Waɗanne matsaloli ne za su iya tasowa sa’ad da iyaye suke tsufa? Me ya sa ya dace ’yan iyali su tattauna da kyau sa’ad da suke so su tsai da shawarar yadda za su kula da iyayensu da suka tsufa? Ta yaya yara za su girmama iyayensu sa’ad da suke kula da su?
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) ia babi na 15 sakin layi na 15-26 da Taƙaitawa da ke shafi na 134
Kammalawa (minti 3 ko ƙasa da hakan)
Waƙa ta 13 da Addu’a