RAYUWAR KIRISTA
Ku Riƙe Amincinku Yayin da Ƙarshe Ya Kusa
MUHIMMANCINSA: Nan ba daɗewa ba, abubuwan ban mamaki za su faru da za su bukace mu mu yi ƙarfin zuciya kuma mu nuna cewa mun dogara ga Jehobah fiye da dā. Ƙunci mai girma zai soma sa’ad da aka hallaka addinin ƙarya. (Mt 24:21; R. Yar 17:16, 17) A lokacin, za mu bukaci ƙarfin zuciya don da alama za mu yi wa’azin hukunci. (R. Yar 16:21) Gog na ƙasar Magog zai kawo mana hari. (Eze 38:10-12, 14-16) Amma Jehobah Mai Iko Duka zai ceci mutanensa ta wurin ‘yaƙi a babbar Ranarsa.’ (R. Yar 16:14, 16) Don mu kasance da ƙarfin zuciya, muna bukatar mu jimre matsalolin da muke fuskanta yanzu.
YADDA ZA MU YI HAKAN:
Ka yi irin rayuwar da Jehobah yake so. —Ish 5:20
Ka ci gaba da ibada tare da ’yan’uwanka Kiristoci.—Ibr 10:24, 25
Ka riƙa bin ja-gorancin ƙungiyar Jehobah. —Ibr 13:17
Ka yi bimbini a kan yadda Jehobah ya ceci mutanensa a dā.—2Bi 2:9
Ka yi addu’a ga Jehobah kuma ka dogara da shi.—Za 112:7, 8
KU KALLI BIDIYON NAN ABUBUWAN DA ZA SU SA MU NUNA ƘARFIN ZUCIYA A NAN GABA—TAƘAITAWA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
Wane gwaji ne masu shelan ikilisiyar nan suka fuskanta sa’ad da aka tura su wasu ikilisiyoyi?
Ta yaya muke kasancewa da ƙarfin zuciya idan muka yi biyayya?
Me ya sa za mu bukaci ƙarfin zuciya a Armageddon?
Ka yi shiri tun yanzu don ka iya kasance da ƙarfin zuciya a nan gaba
Wane labarin Littafi Mai Tsarki ne zai sa mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai iya cece mu?—2Tar 20:1-24