DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | FITOWA 4-5
“Ni Kuwa Zan Bi da Bakinka”
4:10-15
Jehobah ya taimaka wa Musa ya daina jin tsoro. Waɗanne darussa ne za mu koya daga yadda Jehobah ya tattauna da Musa?
Mu daina mai da hankali ga kasawarmu
Mu kasance da tabbacin cewa Jehobah zai taimaka mana mu yi aikinsa
Idan muka dogara ga Allah, ba za mu ji tsoron ’yan Adam ba
Ta yaya Jehobah ya taimaka mini in yi wa’azi duk da matsalolin da nake fuskanta?