DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | FARAWA 36-37
An Wulaƙanta Yusuf Saboda Kishi
37:3-9, 11, 23, 24, 28
Labarin Yusuf ya nuna mana cewa kishi yakan jawo matsaloli da yawa. Ku haɗa nassosin da dalilan da suka sa ya dace mu guji kishin juna.
NASSI
1Sam 18:8, 9
K. Ma 14:30
DALILI
Masu kishi ba za su shiga Mulkin Allah ba
Kishi ba ya jawo salama a ikilisiya
Idan muna kishi, za mu yi ma kanmu lahani
Idan muna kishin mutane, ba za mu ga halayensu masu kyau ba
Waɗanne yanayoyi ne za su iya sa mu ji kishi?