20-26 ga Afrilu
FARAWA 32-33
Waƙa ta 21 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 1)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Ka Yi Kokawa Domin Ka Sami Albarka”: (minti 10)
Fa 32:24—Yakub ya yi kokawa da mala’ika (mwbr20.04-HA an ɗauko daga w03 8/15 25 sakin layi na 3)
Fa 32:25, 26—Yakub ya ci gaba da yin kokawa har sai da ya sami albarka (mwbr20.04-HA an ɗauko daga it-2 190)
Fa 32:27, 28—An albarkaci Yakub domin ya nace (mwbr20.04-HA an ɗauko daga it-1 1228)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 10)
Fa 32:11, 13-15—Ta yaya za mu yi koyi da yadda Yakub ya yi ƙoƙari ya sasanta matsala? (w10 6/15 22 sakin layi na 10-11)
Fa 33:20—Me ya sa Yakub ya kira wani bagade “Allah na Isra’ila”? (mwbr20.04-HA an ɗauko it-1 980)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu game da Jehobah Allah da wa’azi da dai sauransu?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Fa 32:1-21 (th darasi na 5)
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Bidiyon Komawa Ziyara ta Farko: (minti 5) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon. Sai ku amsa tambayoyi na gaba: Ta yaya Na’omi ta koyar da gaskiya? Ta yaya Na’omi da Hannatu suka yi wa’azin tare?
Komawa Ziyara ta Farko: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka bi abin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. (th darasi na 12)
Komawa Ziyara ta Farko: (minti 5 ko ƙasa da hakan) Ka soma da bin abin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. Sai ka gabatar da kuma tattauna (amma kar ka kunna) bidiyon nan Yaya Ake Gudanar da Nazarin Littafi Mai Tsarki? (th darasi na 16)
RAYUWAR KIRISTA
“Me Ya Fi Muhimmanci a Gare Ni?”: (minti 15) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon nan Ka Yi Ƙoƙari Ka Cim ma Makasudan da Ka Kafa.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) ia babi na 6 sakin layi na 15-23 da akwatin da ke shafi na 57 da kuma Taƙaitawa da ke shafi na 58
Kammalawa (minti 3 ko ƙasa da hakan)
Waƙa ta 150 da Addu’a