Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb20 Fabrairu p. 5
  • Yadda Ma’aurata Za Su Karfafa Aurensu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Ma’aurata Za Su Karfafa Aurensu
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Kāre Aurenku
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Zaman Aure
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Aure Kyauta Ne Daga Allah
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Aure, Kyauta ne Daga Allah Mai Kauna
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
mwb20 Fabrairu p. 5
Ibram da Saraya suna shirin barin birnin Ur. Ibram yana rike da babban buhu kuma yana karfafa matarsa Saraya da take saka kaya a kwando.

RAYUWAR KIRISTA

Yadda Ma’aurata Za Su Ƙarfafa Aurensu

Ibrahim da Saratu sun nuna yadda ya kamata ma’aurata su ƙaunaci juna su kuma daraja kansu. (Fa 12:​11-13; 1Bi 3:6) Duk da haka, su ma sun fuskanci matsaloli a aurensu, amma sun jimre sa’ad hakan ya faru. Waɗanne darussa ne ma’aurata za su koya idan suka bincika labarin Ibrahim da Saratu?

Ku riƙa tattaunawa da juna. Zai dace ma’aurata su amsa cikin lumana idan wani cikinsu ya yi magana cikin fushi. (Fa 16:​5, 6) Ya kamata su riƙa keɓe lokaci don su riƙa shakatawa tare. Zai dace su riƙa nunawa ta furucinsu da abubuwan da suke yi cewa suna ƙaunar juna. Mafi muhimmanci ma, zai dace su riƙa nazari da addu’a da ibada tare don Jehobah ya riƙa taimaka musu. (M. Wa 4:12) Idan ma’aurata suka ƙarfafa aurensu, hakan yana ɗaukaka Jehobah wanda ya kafa aure.

KU KALLI BIDIYON NAN YADDA ZA KU ƘARFAFA GAMIN AURE, SA’AN NAN KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • A bidiyon nan, me ya nuna cewa Shaan da Kiara ba sa ba wa juna lokaci kamar yadda suka saba?

  • Me ya sa bai dace ma’aurata su riƙa ɓoye abin da yake damunsu ba?

  • Ta yaya labarin Ibrahim da Saratu ya taimaka wa Shaan da Kiara?

  • Waɗanne matakai ne Shaan da Kiara suka ɗauka don su ƙarfafa aurensu?

  • Me ya sa bai kamata ma’aurata su zata cewa ba za su fuskanci matsaloli a aurensu ba?

Hotunan da aka dauko daga bidiyon ‘Yadda Za Ku Karfafa Gamin Aure.’ Shaan da Kiara sun dauki matakan da suka dace don su karfafa aurensu. 1. Suna zama a kujera daya, amma kowa yana nashi. 2. Sun rike hannayen junansu. 3. Suna wa’azi da farin ciki.

Za ku iya ƙarfafa aurenku!

Don ƙarin bayani a kan yadda za ku ƙarfafa aurenku, ku bincika talifofi na gaba da suka bayyana a Awake! da kuma dandalinmu na jw.org®:

  • “When the Children Are Gone” (Idan Yara Suka Bar Gida)​—g17.4-E 10-11

  • “How to Discuss Problems” (Yadda Za Ku Magance Matsaloli)​—g16.3-E 10-11

  • “When You Are Disappointed With Your Marriage” (Idan Kuka Gaji da Aurenku)​—g-E 3/14 14-15

  • “How to Be a Good Listener” (Yadda Za Ku Riƙa Saurarar Juna da Kyau)​—g-E 12/13 12-13

  • “How to Stop Arguing” (Yadda Za Ku Daina Jayayya da Juna)​—g-E 2/13 4-5

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba