27 ga Janairu–2 ga Fabrairu
FARAWA 9-11
Waƙa ta 101 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 1)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Mutanen Duniya Suna da Yare Ɗaya”: (minti 10)
Fa 11:1-4—Wasu mutane sun yi adawa da Allah ta wajen gina birni da kuma hasumiya (mwbr20.01-HA an ɗauko daga it-1 239; it-2 202 sakin layi na 2)
Fa 11:6-8—Jehobah ya raba yarukansu (mwbr20.01-HA an ɗauko daga it-2 202 sakin layi na 3)
Fa 11:9—Mutanen sun daina aikin ginin kuma suka warwatse (mwbr20.01-HA an ɗauko daga it-2 472)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 10)
Fa 9:20-22, 24, 25—Wane dalili ne wataƙila ya sa Nuhu ya tsine ma Kan’ana maimakon Ham? (mwbr20.01-HA an ɗauko daga it-1 1023 sakin layi na 4)
Fa 10:9, 10—Ta yaya Nimrod ya zama “gwanin farauta . . . [‘da ke hamayya da,’ NW] Yahweh”? (mwbr20.01-HA an ɗauko daga it-2 503)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu game da Jehobah Allah da wa’azi da dai sauransu?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Fa 10:6-32 (th darasi na 5)
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Bidiyon Komawa Ziyara ta Biyu: (minti 5) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon, sai ka yi wa masu sauraro tambayoyi na gaba: Mene ne ya nuna cewa masu shelar sun yi shiri tare kafin su koma ziyarar? Ta yaya ɗan’uwan ya gabatar da ɗaya daga cikin littattafan da muke nazari da su kuma suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki?
Komawa Ziyara ta Biyu: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka bi abin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. (th darasi na 4)
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 5 ko ƙasa da hakan) Ka soma da bin bayanin da aka bayar a kan yadda za a yi koma ziyara ta biyun, sai ka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da littafin nan Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki? (th darasi na 2)
RAYUWAR KIRISTA
“Ka Zama Ƙwararren Ma’aikaci”: (minti 15) Tattaunawa da mai kula da hidima zai yi.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) ia babi na 1 sakin layi na 1-13
Kammalawa (minti 3 ko ƙasa da hakan)
Waƙa ta 56 da Addu’a