20-26 ga Janairu
FARAWA 6-8
Waƙa ta 89 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 1)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Ya Yi Kome Daidai”: (minti 10)
Fa 6:9, 13—Nuhu mutum mai adalci ne amma ya yi rayuwa tare da mutane masu mugunta (w18.02 4 sakin layi na 4)
Fa 6:14-16—An ba wa Nuhu aiki mai wuya sosai (w13 5/1 12 sakin layi na 1)
Fa 6:22—Nuhu ya nuna cewa yana da bangaskiya (w11 9/15 18 sakin layi na 13)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 10)
Fa 7:2—Mene ne tushen bambanci tsakanin dabobbi masu ƙazanta da marasa ƙazanta? (w04 4/1 29 sakin layi na 7)
Fa 7:11—Daga ina ne ruwan da aka yi Rigyawarsa a dukan duniya ya fito? (w04 4/1 30 sakin layi na 1)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu game da Jehobah Allah da wa’azi da dai sauransu?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Fa 6:1-16 (th darasi na 10)
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Bidiyon Komawa Ziyara ta Farko: (minti 5) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon, sai ka tambayi masu sauraro tambayoyi na gaba: Ta yaya mai shelar ta yi amfani da littafin 1 Yohanna 4:8 don ta tattauna da matar? Ta yaya masu shela guda biyun suka haɗa kai don su yi wa matar wa’azi?
Komawa Ziyara ta Farko: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Ka bi bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. (th darasi na 12)
Komawa Ziyara ta Farko: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Ka bi bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. Sai ka ba da ɗaya daga cikin littattafan da muke nazari da su. (th darasi na 7)
RAYUWAR KIRISTA
Ibada ta Iyali: Nuhu Ya Yi Biyayya ga Allah: (minti 10) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon. Sai ku amsa tambayoyin nan: Ta yaya iyayen da ke bidiyon nan suka yi amfani da labarin Nuhu don su koya wa yaransu darussa masu muhimmanci? Wane abu mai kyau ne ka gani a bidiyon nan da za ka so ka yi amfani da shi a ibadarku ta iyali?
Bukatun Ikilisiya: (minti 5)
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) ia karanta Wasiƙa Daga Hukuma da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah da Gabatarwa sakin layi na 1-15
Kammalawa (minti 3 ko ƙasa da hakan)
Waƙa ta 37 da Addu’a