Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb19 Oktoba p. 7
  • Kana Daukan Littafi Mai Tsarki da Daraja Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kana Daukan Littafi Mai Tsarki da Daraja Kuwa?
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
  • Makamantan Littattafai
  • Sun Dauki Littafi Mai Tsarki da Muhimmanci—Gajeren Bidiyo na Labarin (William Tyndale)
    Karin Batutuwa
  • Sun Dauki Littafi Mai Tsarki da Muhimmanci
    Karin Batutuwa
  • Dandalinmu na Intane—An Tsara Shi Ne don ’Yan’uwa da Kuma Wasu Su Amfana
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Kuna Bincika JW.ORG/HA don Samun Shawarwari na Yau da Kullum?
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
mwb19 Oktoba p. 7

RAYUWAR KIRISTA

Kana Ɗaukan Littafi Mai Tsarki da Daraja Kuwa?

Jehobah ne Mawallafin Littafi Mai Tsarki, shi ya sa Littafi Mai Tsarki yake koya mana ra’ayin Jehobah game da abubuwa. (2Bi 1:​20, 21) Littafi Mai Tsarki ya nanata yadda Mulkin Allah zai nuna cewa Jehobah ne kaɗai ya cancanci ya yi sarauta kuma ’yan Adam za su ji daɗin rayuwa nan ba da daɗewa ba. Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya bayyana mana halaye masu kyau na Ubanmu Jehobah.​—Za 86:15.

Dukanmu muna da dalilin da ya sa muke ɗaukan Littafi Mai Tsarki da daraja sosai. Amma za mu fi nuna cewa muna daraja shi idan muna karanta da kuma bin shawarwarinsa. Bari ayyukanmu su nuna cewa mun amince da abin da marubucin zabura ya ce: “Ina misalin ƙaunata ga Koyarwarka!”​—Za 119:97.

KU KALLI BIDIYON NAN SUN ƊAUKI LITTAFI MAI TSARKI DA MUHIMMANCI​—GAJEREN BIDIYO NA LABARIN (WILLIAM TYNDALE), SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • William Tyndale; William Tyndale a inda yake buga littafi; Kofin Sabon Alkawari da Tyndale ya fara fassarawa

    Me ya sa William Tyndale ya fassara wani sashe na Littafi Mai Tsarki?

  • Me ya sa fassara Littafi Mai Tsarki da Tyndale ya yi ba ƙaramin aiki ba ne?

  • Ta yaya aka kai Littafi Mai Tsarki da Tyndale ya fassara zuwa Ingila?

  • Ta yaya kowannenmu zai nuna cewa yana daraja Littafi Mai Tsarki?

DON BIMBINI: Ta yaya Kalmar Allah take kama da . . .

  • fitila da kuma haske?​—Za 119:105

  • ruwa?​—Afi 5:26

  • takobi?​—Afi 6:17

  • madubi?​—Yak 1:​23-25

KA KARANTA KALMAR ALLAH KOYAUSHE

Schedule for Bible Reading

Ka taɓa amfani da tsari na karatun Littafi Mai Tsarki, wato Schedule for Bible Reading da ke dandalinmu na jw.org? Idan ka sauƙar da shi, zai kai ka nassin da kake so ka karanta a dandalinmu na jw.org kai tsaye. Idan akwai sautin karatun a yarenku, za ka iya ganinsa a jw.org.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba