DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | TITUS 1–FILIMON
“Ka Kuma Naɗa Dattawa”
An ba wa Titus hakkin “naɗa dattawa a kowane gari.” Wannan tsarin ne masu kula da da’ira suke bi sa’ad da suke naɗa dattawa a ikilisiya.
HUKUMAR DA KE KULA DA AYYUKANMU
Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta bi tsarin Kiristocin ƙarni na farko wajen ba wa masu kula da da’ira hakkin naɗa dattawa da kuma bayi masu hidima.
MASU KULA DA DA’IRA
Kowanne mai kula da da’ira zai yi addu’a sosai a kan abubuwan da dattawa suka gaya masa game da ’yan’uwan don ya san ko sun cancanta a naɗa su.
’YAN’UWAN DA AKA NAƊA SU DATTAWA
Dole ne dattawan su ci gaba da kasancewa da halayen da suka jitu da Kalmar Allah bayan an naɗa su.