1-7 ga Yuli
KOLOSIYAWA 1-4
Waƙa ta 56 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Ku Kawar da Halinku na Dā, Sai Ku Yafa Sabon Hali”: (minti 10)
[Ku kalli bidiyon Gabatarwar Littafin Kolosiyawa.]
Kol 3:5-9—‘Ku kawar da halinku na dā’ (w11 3/15 10 sakin layi na 12-13)
Kol 3:10-14—Sai ku yafa “sabon halin nan” (w13 9/15 21 sakin layi na 18-19)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
Kol 1:13, 14—Mene ne “mulkin Ɗansa wanda yake ƙauna”? (mwbr19.07-HA an ɗauko daga it-2 169 sakin layi na 3-5)
Kol 2:8—Mene ne “ikon ruhohi na duniya”? (w08 8/15 28 sakin layi na 9)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Kol 1:1-20 (th darasi na 2)
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Ka Mai da Hankali ga Karatu da Kuma Koyarwa: (minti 10) Tattaunawa. Ka saka bidiyon nan Ka Koyar da Gaskiya, bayan haka sai ku tattauna darasi na 7 a ƙasidar nan Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa.
Jawabi: (minti 5 ko ƙasa da hakan) w04 5/1 27-28 sakin layi na 3-7—Jigo: Ta Yaya Wasu Kiristoci Suka “Zama Abin Ta’aziyya [Ƙarfafa]” ga Bulus? (Kol 4:11) (th darasi na 7)
RAYUWAR KIRISTA
Rahoton Kwamitin Koyarwa na 2018: (minti 15) Ku kalli bidiyon. Sai ku amsa tambayoyi na gaba: Ta yaya ƙungiyarmu take tafiye-tafiye don ta yi ayyukanta? Ta yaya Sashen Tafiye-Tafiye na hedkwatarmu take taimaka wajen rage kuɗaɗen da ƙungiyarmu take kashewa? Mene ne ’yan’uwa za su yi don su rage kuɗaɗen da ƙungiyarmu take kashewa? Ta yaya Sashen Tafiye-Tafiye na hedkwatarmu take taimaka wa ’yan’uwa da za su je taron Shaidun Jehobah na ƙasashe da za a yi a 2019?
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) bhs babi na 10 sakin layi na 1-9 da Ƙarin Bayani na 8
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 102 da Addu’a