Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb19 Yuni p. 8
  • Ka Yi Nazari A Hanyar da Za Ka Amfana Sosai

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Nazari A Hanyar da Za Ka Amfana Sosai
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
  • Makamantan Littattafai
  • Nazari Mai Albarka Kuma Mai Daɗi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ka Bi Tafarkin Sarakuna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ka More Nazarinka Na Kalmar Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Yaya Shaidun Jehobah Suke Nazarin Littafi Mai Tsarki da Mutane?
    Tambayoyin da Ake Yawan Yi
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
mwb19 Yuni p. 8

RAYUWAR KIRISTA

Ka Yi Nazari A Hanyar da Za Ka Amfana Sosai

MUHIMMANCINSA: Yin nazari zai taimaka mana mu fahimci faɗi da tsawo da girma da kuma zurfin Kalmar Allah. (Afi 3:18) Ƙari ga haka, yana taimaka mana mu zama masu adalci ba waɗanda suka ɓata kansu a duniyar nan ba, amma waɗanda suke “riƙe da maganar rai kankan.” (Fib 2:​15, 16, Littafi Mai Tsarki) Nazarin Littafi Mai Tsarki yana ba mu damar zaɓan littafin da za mu yi nazarinsa da ya yi daidai da yanayinmu. Me za mu yi don mu amfana sosai sa’ad da muke karatu da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki?

YADDA ZA MU YI HAKAN:

  • Ka riƙa saka maki ko ka yi rubutu a Littafi Mai Tsarkin da kake amfani da shi ko da kana amfani da na na’ura ce

  • Sa’ad da kake karanta Littafi Mai Tsarki, ka riƙa yin waɗannan tambayoyin: ‘Mene ne? Me ya sa? Yaushe? Yaya? A ina? Waye?’

  • Ka bincika sosai. Ka yi amfani da kayan bincike kuma ka rubuta jigon ko ayar sa’ad da kake binciken

  • Ka yi tunani sosai a kan abin da ka karanta don ka fahimci darussan da za ka koya daga karatun da ka yi

  • Ka yi amfani da abin da ka koya a rayuwarka ta yau da kullum.​—Lu 6:​47, 48

KU KALLI BIDIYON NAN KU “RIƘE KALMAR RAI SOSAI” TA WURIN YIN NAZARI DA KYAU, BAYAN HAKA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Ta yaya wasu suka kwatanta yin nazari?

  • Me ya sa ya dace mu soma nazari da addu’a?

  • Me zai taimaka mana mu fahimci nassosin Littafi Mai Tsarki da kyau?

  • Ta yaya ya kamata mu saka maki a Littafi Mai Tsarkin da muke amfani da shi?

  • Me ya sa yin bimbini yake da muhimmanci sa’ad da muke nazarin Littafi Mai Tsarki?

  • Me ya kamata mu yi da abin da muka koya?

Wata ’yar’uwa tana nazarin Littafi Mai Tsarki da kyau; wani dan’uwa yana saka maki a Littafi Mai Tsarkinsa; wata ’yar’uwa tana gaya ma wasu mutane biyu darussan da ta koya a Littafi Mai Tsarki; wani dan’uwa yana addu’a

“Ina misalin ƙaunata ga Koyarwarka! Dukan yini ita ce tunanina.”​—Za 119:97

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba