DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | 2 KORINTIYAWA 11-13
Abin da Ya Zama Kamar ‘Ƙaya a Jikin’ Bulus
A Littafi Mai Tsarki, akan yi amfani da ƙaya wajen kwatanta mutane masu fitina ko abin da zai iya ji wa mutum rauni. (L.Ƙi 33:55; K. Ma 22:5; Eze 28:24) Sa’ad da Bulus ya yi magana a kan ‘ƙaya a jikinsa,’ wataƙila yana magana ne a kan manzannin ƙarya da suka ƙi gaskata cewa shi manzo ne kuma suke sūkar aikin da yake yi. Ga ƙarin wasu abubuwa da wataƙila Bulus yake nufi a nassosin nan sa’ad da ya ce yana da ƙaya a jikinsa.
Wace ƙaya ce kake fama da ita a jikinka?
Ta yaya za ka dogara ga Jehobah don ya taimaka maka ka jimre?