RAYUWAR KIRISTA
Ƙauna Ce Alamar Kiristoci Na Gaskiya—Ku Guji Son Kai da Saurin Fushi
ME YA SA YAKE DA MUHIMMANCI: Yesu ya ce ƙauna ce za ta sa a san mabiyansa na gaskiya. (Yoh 13:34, 35) Idan muna so mu ƙaunaci ’yan’uwanmu kamar yadda Kristi ya yi, dole ne mu yi abin da zai faranta musu rai kuma mu guji yin fushi a kowane lokaci.—1Ko 13:5.
YADDA ZA MU YI HAKAN:
Idan wani ya ɓata mana rai, mu tsaya mu yi tunani a kan dalilin da ya sa ya yi hakan da kuma abin da zai iya faruwa idan muka yi magana da fushi.—K. Ma 19:11
Mu tuna cewa dukanmu ajizai ne kuma mukan faɗi ko yi abin da za mu yi da-na-saninsa daga baya
Mu riƙa sasanta matsaloli da sauri
KU KALLI BIDIYON NAN “KU KAUNACI JUNA”—KU GUJI SON KAI DA SAURIN FUSHI, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:
Mene ne Larry ya yi sa’ad da Tom ya gaya masa wani abu?
Ta yaya tunanin da Tom ya yi, ya taimaka masa ya guji saurin fushi?
Me ya faru bayan da Tom ya amsa ma Larry a hankali?
Ta yaya ’yan’uwa a ikilisiya za su amfana idan wani ya ɓata mana rai kuma muka kame kanmu?