RAYUWAR KIRISTA
Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Yadda Za Mu Yi Amfani da JW.ORG
MUHIMMANCINSA: Dukan littattafai da muke wa’azi da su suna gabatar da dandalin jw.org ga mutane. Ainihin dalilin da ya sa aka wallafa katin jw.org da kuma warƙar nan A Ina Za Mu Iya Samun Amsoshin Muhimman Tambayoyi Game da Rayuwa? shi ne don a gabatar da dandalin jw.org ga mutane. Za ka iya yin amfani da dandalin jw.org don ka saukar da ɗaya daga cikin littattafanmu kuma ka aika ma wani ta imel ko kuma ka aika masa adireshin. Hakan yana da kyau musamman ma in kana wa’azi ga wanda yake wani yare dabam. Ban da haka, mutane za su iya yi maka tambaya da babu amsoshinsu a littattafan da muke wa’azi da su, amma akwai a dandalin jw.org. Idan mun iya amfani da dandalin, zai taimaka mana sosai a wa’azin da muke yi.
YADDA ZA MU YI HAKAN:
Ka yi amfani da sashen “KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI.” Idan kana tattaunawa da iyayen da suke so su san yadda za su reni yaransu, ka shiga sashen KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI > AURE DA ZAMAN IYALI.
Ka yi amfani da sashen “LITTATTAFAI.” Idan kana tattaunawa da ɗan ajinku a makaranta kuma kana so ka nuna masa ƙasidar nan Amsoshi ga Tambayoyi 10 da Matasa Suke Yi, ka shiga sashen LITTATTAFAI > LITTATTAFAI DA ƘASIDU.
Ka yi amfani da sashen “GAME DA MU.” Idan kana tattaunawa da wani ma’aikaci da yake so ya san game da imaninmu cikin hanzari, ka shiga sashen GAME DA MU > TAMBAYOYIN DA AKE YAWAN YI GAME DA SHAIDUN JEHOBAH.
KU KALLI BIDIYON NAN YADDA AKE AMFANI DA DANDALIN JW.ORG, SAI KU LURA DA INDA ZA KU SHIGA A DANDALIN DON KU TAIMAKA MA:
mutumin da bai yarda da wanzuwar Allah ba
mutumin da bala’i ya afka masa
ɗan’uwa ko ’yar’uwa da suka daina fita wa’azi
mutumin da ka ziyarce shi kuma yana son ya san yadda muke samun kuɗi da muke amfani da shi a ƙungiyarmu
mutumin da ke wata ƙasa, amma yana son ya halarci taro idan ya koma ƙasarsu