Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb18 Yuni p. 2
  • Ku Bi Yesu Sawu da Kafa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Bi Yesu Sawu da Kafa
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Yi Farin Ciki Idan Ana Tsananta Muku
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
  • Za Mu Amfana Idan Muka Jimre Wahala
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Za Ka Iya Jimre Tsanantawa
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Yadda Jehobah Yake Taimaka Mana Mu Jimre
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
mwb18 Yuni p. 2

RAYUWAR KIRISTA

Ku Bi Yesu Sawu da Ƙafa

Yesu ya kafa mana misali mai kyau da za mu iya bi musamman idan muna fuskantar matsaloli ko kuma tsanani. (1Bi 2:​21-23) Ko da yake an zazzagi Yesu, bai rama ba har ma a lokacin da yake shan wahala. (Mk 15:​29-32) Me ya taimaka masa ya jimre? Ya ƙudura zai yi nufin Jehobah shi ya sa ya jimre. (Yoh 6:38) Ban da haka ma, ya mai da hankali ga “farin cikin da aka sa a gabansa.”​—Ibr 12:2.

Me za mu yi idan aka wulaƙanta mu saboda imaninmu? Kiristoci na gaskiya ba sa ‘sāka wa mutane da mugunta.’ (Ro 12:​14, 17) Idan muka yi koyi da abin da Yesu ya yi sa’ad da yake shan wahala, za mu yi farin ciki cewa Allah yana amincewa da ibadarmu.​—Mt 5:​10-12; 1Bi 4:​12-14.

KU KALLI BIDIYON NAN SUNAN JEHOBAH YA FI MUHIMMANCI, BAYAN HAKA, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Ta yaya ’Yar’uwa Pötzingera ta yi amfani da lokacinta da kyau sa’ad da aka tsāre ta?

  • Wace irin wahala ce Ɗan’uwa da ’Yar’uwa Pötzinger suka jimre sa’ad da suka yi zama a sansani dabam-dabam?

  • Me ya taimaka musu su jimre?

Yadda mata suke yin ayyuka masu wuya a lokacin da ’yan Nazi suka saka Shaidu a kurkuku; Dan’uwa da ’Yar’uwa Pöetzinger

Ku bi Yesu sawu da ƙafa sa’ad da kuke shan wahala

a Za a iya rubuta sunar kamar haka Poetzinger.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba