DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | DANIYEL 10-12
Jehobah Ya Annabta Sarakunan da Za Su Yi Mulki
11:2
Sarakuna huɗu za su taso a Farisa. Na huɗun zai sa “dukan mutane su tayar ma mulkin Hellas.”
Sairus Mai Girma
Cambyses na Biyu
Darius na Ɗaya
Xerxes na Ɗaya (da ake zato shi ne Sarki Ahasuerus da ya auri Esther)
11:3
Sarki mai iko zai sarauci Hellas kuma zai mulki ƙasashe da yawa.
Iskandari Mai Girma
11:4
Za a raba mulkin Hellas waje huɗu kuma a rarraba wa janarorin Iskandari guda huɗu.
Cassander
Lysimachus
Seleucus na Ɗaya
Ptolemy na Ɗaya