DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | EZEKIYEL 32-34
Hakkin da Mai Tsaro Yake da Shi
Masu tsaro suna tsayawa a kan ganuwar birni don su sanar da mutanen da ke cikin gari game da haɗarin da ke tafe. Jehobah ya ba Ezekiyel matsayin “mai-tsaro ga gidan Isra’ila.”
33:7
Ezekiyel ya gaya wa Isra’ilawa cewa za a hukunta su idan ba su daina mugunta ba
Wane saƙon Jehobah ne muke yin shelarsa a yau?
33:9, 14-16
Ezekiyel zai iya ceton ransa da kuma na mutane idan ya yi shelar saƙon
Me ya kamata ya motsa mu mu yi shelar saƙon da Jehobah ya ba mu da gaggawa?