DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | IRMIYA 51-52
Maganar Jehobah Tana Cika a Koyaushe
Jehobah ya annabta abin da zai faru a nan gaba
Maharbin da ke tsaron fādar Fasiya
“Ku tsinana kibawu”
51:11, 28
Mutanen Midiya da Fasiya ƙwararrun maharba ne kuma kibiya ce ainihin makaminsu. Don haka, sun watsa kibawunsu don su yi tsini sosai
Sojojin “Babila sun ƙi yaƙi”
51:30
Allon Nabonidus Chronicle ya ce: “Sojojin Sairus sun halaka Babila ba tare da yin yaƙi ba.” Ba su yi yaƙin fito-na-fito ba kuma hakan ya jitu da annabcin Irmiya
Allon Nabonidus Chronicle
‘Babila za ta zama tullan ƙasa da kuma kango har abada’
51:37, 62
Ɗaukakar Babila ta soma ragewa a shekara ta 539. Iskandari Mai Girma ya so ya mai da Babila babban birninsa, amma ya mutu babu zato. A lokacin da aka fara samun Kiristoci, da akwai wasu Yahudawa da suke zama a Babila kuma hakan ne ya sa Bitrus ya je wajen. Amma a ƙarni na huɗu, mutane sun daina zama a ƙasar gabaki ɗaya