DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | IRMIYA 49-50
Jehobah Yana Sāka wa Masu Sauƙin Kai Kuma Yana Hukunta Masu Girman Kai
50:4-7
Isra’ilawan da suka tuba za su yi matuƙar farin ciki sa’ad da Jehobah ya ceto su daga bauta
Za su sake yin yarjejeniya da shi kuma su koma Urushalima don su soma bauta ta gaskiya
50:29, 39
Jehobah zai hukunta Babiloniyawa masu girman kai don yadda suka wulaƙanta bayinsa
Mutane sun daina zama a Babila daidai yadda aka annabta