Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb17 Afrilu p. 2
  • Ku Marabce Su da Kyau

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Marabce Su da Kyau
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
  • Makamantan Littattafai
  • Za a Ba da Shaida Sosai
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Ku Marabci Bakin da Suka Hallara
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
  • Ku Marabce Su!
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Ta Yaya Za Ka Saba da Sabuwar Ikilisiyar da Ka Je?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
mwb17 Afrilu p. 2

RAYUWAR KIRISTA

Ku Marabce Su da Kyau

Su wane ne za mu marabtar da kyau? Duka sababbin mutanen da suka zo taronmu da kuma waɗanda suka daɗe ba su halarci taro ba. (Ro 15:7; Ibr 13:2) Ko ‘yan’uwanmu da suka zo daga wata ƙasa ko kuma waɗanda suka yi shekaru da yawa ba su zo taro ba. Idan kai ne a irin wannan yanayin, yaya za ka ji in aka marabce ka da kyau? Za ka yi farin ciki sosai ko ba haka ba? (Mt 7:12) Don haka, zai yi kyau ka gaisa da mutane a Majami’ar Mulki kafin a soma taro da kuma bayan an gama taro. Hakan yana ƙara sa mu jin daɗin taro sosai kuma yana ɗaukaka Jehobah. (Mt 5:16) Wataƙila ba zai yiwu mu gaisa da kowa ba. Amma mutane za su yi farin ciki idan muka yi iya ƙoƙarinmu don mu gaishe su.a

Ba sai a taron Tunawa da Mutuwar Yesu ne kawai za mu marabci mutane da kyau ba. Amma muna bukatar yin hakan a kowane lokaci. Idan sababbi suka ga yadda muke ƙaunar juna, hakan zai motsa su su ɗaukaka Jehobah kuma su soma bauta masa.​—Yoh 13:35.

a Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki sun hana mu gaisawa da waɗanda aka yi musu yankan zumunci da suka halarci taro.​—1Ko 5:11; 2Yo 10.

Wani dan’uwa yana marabtar wani bako zuwa Majami’ar Mulki

YADDA ZA MU IYA TAIMAKA WA SABABBI

  • Ka gaya musu sunanka kuma ka tambaye nasu sunan

  • Ka ce su zauna da kai

  • Ka bar su su yi amfani da naka Littafi Mai Tsarki da littafin waƙoƙi

  • Bayan an gama taron, ka tambaye su ko suna da tambaya

  • Ka tambaye su ko suna so a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba