Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb16 Oktoba p. 8
  • Kana Yin Amfani da Katin JW.ORG Yadda Ya Dace Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kana Yin Amfani da Katin JW.ORG Yadda Ya Dace Kuwa?
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Yi Amfani da Shafin Farko na JW.ORG Yayin da Kuke Waꞌazi
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi​—Yadda Za Mu Yi Amfani da JW.ORG
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
  • Abubuwan da Mulkin Allah Ya Cim ma a Cikin Shekara Dari
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • A Ina Ne Za Mu Sami Amsoshin Muhimman Tambayoyi?
    A Ina Ne Za Mu Sami Amsoshin Muhimman Tambayoyi?
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
mwb16 Oktoba p. 8

RAYUWAR KIRISTA

Kana Yin Amfani da Katin JW.ORG Yadda Ya Dace Kuwa?

Wani Mashaidin Jehobah yana ba wani mutum katin jw.org

Da yake muna gab da ƙunci mai girma, ya kamata mu yi wa’azi da ƙwazo. (Mis 24:11, 12, 20) Za mu iya yin amfani da katin jw.org don mu taimaka wa mutane su karanta Kalmar Allah. Katin na ɗauke da wata alama da za a iya yin scan don a ga bidiyon nan Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki? da kuma yadda za a sami ƙarin bayani ko soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Wasu mutane ba sa karɓan mujallunmu amma suna son su shiga dandalinmu. Kada mu ɓata lokaci wajen ba su katin jw.org. Amma bai kamata mu ba mutanen da ba sa son saƙonmu katin ba.

Yayin da muke sha’aninmu na yau da kullum, muna iya soma tattaunawa da mutane ta wajen ce musu: “Zan so in ba ka wani abu. Wannan katin zai kai ka dandalinmu da ke ɗauke da bayanai da kuma bidiyoyin da suka tattauna batutuwa da yawa.” (Yoh 4:7) Da yake katin jw.org bai da girma, za ka iya ɗaukansa da ɗan yawa don ka ba mutane sa’ad da ka sami damar yin hakan.

KA BA DA KATIN JW.ORG . . .

  • sa’ad da kake harkokinka na yau da kullum

  • sa’ad da kake wa’azi a yankin da ake kasuwanci

  • sa’ad da wani ya so saƙonmu amma ya ƙi ya karɓi littafi ko kuma mujalla

Katin jw.org da ke dauke da Baibul da ke a bude
Katin jw.org da ya nuna yadda wani Mashaidin Jehobah yake karanta wa wani mutum Baibul
Katin jw.org da ya nuna yadda wani Mashaidin Jehobah yake nazarin Baibul da wata iyali
Bayan katin jw.org

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba