Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb16 Janairu p. 2
  • Gatan Gina da Kuma Gyara Wuraren Ibadarmu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Gatan Gina da Kuma Gyara Wuraren Ibadarmu
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ZA MU IYA TAIMAKAWA TA WAJEN . . .
  • Wannan Wurin Ne Muke Bauta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Aikin Gini da Ke Ɗaukaka Jehobah
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
  • Yaya Za Mu Taimaka Wajen Kula da Majami’ar Mulki?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
  • Anini Biyu
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
mwb16 Janairu p. 2

RAYUWAR KIRISTA

Gatan Gina da Kuma Gyara Wuraren Ibadarmu

Gina haikali a zamanin Isra’ilawa ya bukaci aiki tuƙuru da kuma kuɗi mai yawa. Duk da haka, Isra’ilawa sun yi aikin da ƙwazo. (1Lab 29:​2-9; 2Lab 6:​7, 8) Gyare-gyaren da Isra’ilawa suka yi a haikalin bayan sun kammala ginin ya nuna ko suna da dangantaka mai kyau da Jehobah ko babu. (2Sa 22:​3-6; 2Lab 28:24; 29:⁠3) A yau, Kiristoci ma suna sa ƙwazo wajen gina da tsabtace da kuma gyara Majami’un Mulki da kuma Majami’un Manyan Taro. Yin irin waɗannan ayyukan ga Jehobah babban gata ne sosai kuma hakan ibada ce.​—⁠Za 127:1; R. Yoh 7:⁠15.

ZA MU IYA TAIMAKAWA TA WAJEN . . .

  • Tsabtace cikin Majami’ar Mulki

    Tsabtace wuri bayan kowane taro. Idan ba za ka iya yin shara ba saboda yanayinka, ka kwashe duk wani datti da ke kewaye da kai.

  • Share Majami’ar Mulki

    Ba da kai a duk lokacin da ake share ko gyara Majami’ar Mulki. Idan mutane da yawa suka ba da kai wajen yin aikin, za a ji daɗi kuma aikin zai yi sauƙi.​—⁠lv 92-93 sakin layi na 18.

  • Saka kudi cikin akwatin ba da gudummawa

    Ba da gudummawar kuɗi. Ko da kuɗin da muke da shi ba yawa, Jehobah yana farin ciki da waɗanda suke bayarwa da zuciya ɗaya.​—⁠Mk 12:​41-44.

  • Gyara wurin ibada

    Ba da kai wajen gina da kuma gyara wuraren da muke ibada, idan zai yiwu. Ba sai ka iya gini ba ne za ka iya ba da kai.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba