Tambayoyin Masu Shela
◼ A Wane Lokaci Ne Zai Dace Ka Dakatar da Nazari da Ɗalibinka?
Idan ka ɗago cewa ɗalibinka ba ya so ya sami ci gaba, zai dace ka yi amfani da basira don dakatar da nazarin. (Mat. 10:11) Ka yi la’akari da waɗannan tambayoyin: Shin ɗalibin yana yarda ku yi nazari? Yana shirya littafin kafin nazarin kuwa? Ya taɓa halartar taronmu kuwa? Yana gaya wa wasu abin da yake koya? Yana canja salon rayuwarsa ya jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuwa? Hakika, ya kamata mu yi la’akari da shekarunsa da iliminsa, muna tuna cewa yadda kowane mutum yake samun ci gaba ya bambanta sosai. Kuma, idan kuka dakatar da nazarin, za ku iya gaya masa cewa, a duk lokacin da ya shirya, za ku ci gaba da nazarin.—1 Tim. 2:4.