Tsarin Ayyuka na Makon 7 ga Disamba
MAKON 7 GA DISAMBA
Waƙa ta 86 da Addu’a
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
ia babi na 4 sakin layi na 1-15, da akwatin da ke shafi na 39 (minti 30)
Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 2 Labarbaru 10-14 (minti 8)
Na 1: 2 Labarbaru 13:13-22 (minti 3 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Me Ya Sa Wajibi Ne Mu Riƙa Tuna Cewa Lokaci Ya Ƙure ma Wannan Duniyar? (minti 5)
Na 3: Sarautar Wa Za Ta Sa ’Yan Adam Su Mori Irin Jin Daɗi da Zaman Lafiya da Aka More Tun Asali?—wp14 7/1 16 sakin layi na 1-4 (minti 5)
Taron Hidima:
JIGON WATA: “Sai ta wurin wahala da yawa za mu shiga Mulkin Allah.”—A. M. 14:22.
Waƙa ta 85
Minti 10: “Sai ta Wurin Wahala da Yawa Za Mu Shiga Mulkin Allah.” Jawabin da zai bayyana jigon wata. Ka karanta da kuma tattauna Ayyukan Manzanni 14:21, 22 da kuma 1 Bitrus 4:12-14. (Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Satumba, 2014, shafi na 13, sakin layi na 3-6.) Ka ɗan faɗi wasu abubuwan da za a tattauna a Taron Hidima na wannan watan kuma ka nuna yadda suke da alaƙa da jigon. Ka ƙarfafa ’yan’uwa su kalli bidiyon nan Dukan ’Yan’uwanmu a Faɗin Duniya don Taron Hidima da za a yi mako mai zuwa.
Minti 10: Yaya Ya Kamata Ka Ba da Amsa? (Kol. 4:6) Jawabin da aka ɗauko daga Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Mayu, 2014, shafi na 12, sakin layi na 5-8. Ka sa a yi gwaji guda biyu. A gwaji na farko, wani maigida ya yi wa mai shela baƙar magana, mai shelan ma ya amsa da fushi, kuma hakan ya sa bai saurari saƙon ba. A gwaji na biyu, bayan maigidan ya yi masa baƙar magana, sai mai shelan ya ɗan dakata, ya yi magana da fara’a, kuma hakan ya sa maigidan ya saurare shi.
Minti 10: “Ku Bi Gurbin Annabawa—Habakkuk.” Tambayoyi ana ba da amsoshi.
Waƙa ta 74 da Addu’a