Tsarin Ayyuka na Makon 12 ga Oktoba
MAKON 12 GA OKTOBA
Waƙa ta 135 da Addu’a
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl babi na 31 sakin layi na 21-23, da akwatin da ke shafi na 319 (minti 30)
Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 1 Labarbaru 5-7 (minti 8)
Na 1: 1 Labarbaru 6:48-60 (minti 3 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Wane Ne Zai Kawo Zaman Lafiya a Duniya?—wp13 7/1 16 sakin layi na 1-4 (minti 5)
Na 3: Abin da Ya Sa Littafi Mai Tsarki Ya Yi Mana Gargaɗi a Kan “Cika Yin Adalci”—M. Wa. 7:16 (minti 5)
Taron Hidima:
JIGON WATA: Ku zama “dasassu” da kuma ‘kafaffu cikin bangaskiya.’—Kol. 2:6, 7.
Waƙa ta 117
Minti 10: Ku Zama “Dasassu” da Kuma ‘Kafaffu Cikin Bangaskiya.’ Jawabin da zai bayyana jigon watan. Mene ne ake nufi da zama dasassu da kuma kafaffu cikin bangaskiya, kuma ta yaya za mu yi hakan? (Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Oktoba, 2009, shafi na 26-28.) Ka karanta da kuma tattauna Kolosiyawa 2:6, 7 da Ibraniyawa 6:1 da kuma Yahuda 20, 21. Ka ɗan faɗi wasu abubuwa da za a tattauna a Taron Hidima na wannan watan kuma ka nuna yadda suke da alaƙa da jigon.
Minti 20: “Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Ka Koya wa Ɗalibanka Yin Nazari.” Tattaunawa. Ka sa a yi gwajin da ya nuna wani mai shela da ya ƙware yana nuna wa ɗalibinsa yadda zai yi amfani da Littafin Bincike Don Shaidun Jehobah wajen amsa wata tambaya da aka yi masa game da Littafi Mai Tsarki.
Waƙa ta 116 da Addu’a