Sanarwa
Littattafan da za mu ba mutane a watan Yuni: Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ko Za Ka so ka San Amsoshin Waɗannan Tambayoyin? Idan ba ku da su, ku ba da ƙasidar nan Albishiri Daga Allah! Yuli da Agusta: Ku ba da ɗaya daga cikin ƙasidun nan masu shafuffuka 32: Allah Yana Kula Da Mu Kuwa Da Gaske?, Ka Saurari Allah, Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada, Hanyar Rai Madawwami—Ka Same ta Kuwa?, Minene Yakan Faru Mana Sa’anda Muka Mutu?, Minene Ma’anar Rai?—Ina Yadda Zaka Same Shi?, Za Ka Iya Zama Abokin Allah! Satumba: Mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake!
◼ Ku rubuta adadin dukan warƙoƙi da kuma takardun gayyata da kuka ba mutane ko kuma kuka bari a baƙin ƙofa sa’ad da kuke ba da rahoton wa’azi a ƙarshen wata. Kuma ku rubuta hakan a inda aka rubuta “Brochures and Tracts” (Ƙasidu da Warƙoƙi). Idan wani ya nuna yana son saƙonmu kuma ya karɓi littafi ko warƙa, ku yi ƙoƙari ku koma ziyara wurinsa.
◼ Za a soma nazarin littafin nan Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu a Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya a makon 19 ga Oktoba, 2015. Ikilisiyoyin da suke bukatar ƙarin kofofi na littafin su ce a turo musu. ’Yan’uwan da suka fi so a na’urarsu su saukar da shi daga dandalin jw.org/ha maimakon su karɓi wanda aka buga.