Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 4/15 p. 3
  • Bitar Makarantar Hidima ta Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Bitar Makarantar Hidima ta Allah
  • Hidimarmu Ta Mulki—2015
Hidimarmu Ta Mulki—2015
km 4/15 p. 3

Bitar Makarantar Hidima ta Allah

Za a tattauna tambayoyin da ke gaba a Makarantar Hidima ta Allah a makon 27 ga Afrilu, 2015. An saka kwanan watan da za a tattauna waɗannan bayanan domin ku yi bincike sa’ad da kuke shirya makaranta kowane mako.

  1. Ta yaya Ruth ta cika alkawarinta? (Ruth 1:10) [2 ga Maris, w12 10/15 shafi na 29 sakin layi na 9]

  2. Labarin Naomi ya koya maka wane darasi ne game da muhimmancin dogara ga Allah? (Ruth 4:14-17) [2 ga Maris, w08 2/15 shafi na 5 sakin layi na 15]

  3. Me ya sa Hannatu ta yi addu’a cewa Jehobah ya “ba sarkinsa iko” alhali babu ɗan Adam da ke sarauta bisa Isra’ila a lokacin? (1 Sam. 2:10) [9 ga Maris, w05 4/1 shafi na 7 sakin layi na 3]

  4. Shin Sama’ila ya yi barci a wuri Mafi Tsarki ne? (1 Sam. 3:3) [9 ga Maris, w05 4/1 shafi na 7 sakin layi na 4]

  5. Mene ne za mu iya koya daga yadda Saul ya ƙi ya ɗauki fansa sa’ad da wasu “mutanen Belial” suka ƙi su miƙa wuya ga sarautarsa? (1 Sam. 10:22, 27) [23 ga Maris, w05 4/1 shafi na 8 sakin layi na 6]

  6. Me ya sa Saul ya yi kuskure sa’ad da ya ɗauka cewa mutum zai iya ba da hadaya a maimakon ya yi biyayya ga Jehobah? (1 Sam. 15:22, 23) [30 ga Maris, w07 7/1 shafi na 18 sakin layi na 3-4]

  7. Me ya sa yake da ban ƙarfafa mu san cewa Jehobah yana “duban zuciya?” (1 Sam. 16:7) [6 ga Afrilu, w10 7/1 shafi na 15 sakin layi na 7]

  8. A Misalai 1:4, wace baiwa ce muke da shi da Jehobah yake so mu yi amfani da shi sa’ad da muke fuskantar yanayi masu wuya? (1 Sam. 21:12, 13) [13 ga Afrilu, w05 4/1 shafi na 9 sakin layi na 7]

  9. Me ya sa za mu iya cewa ba taurin kai ba ne Abigail ta yi sa’ad da ta ba Dauda da mutanensa abinci? (1 Sam. 25:10, 11, 18, 19) [20 ga Afrilu, w09 7/1 shafi na 24 sakin layi na 4]

  10. Me ya sa neman gafara domin laifin da Abigail ba ta yi ba hikima ce da tawali’u a gare ta, kuma ta yaya za mu amfana daga misalinta? (1 Sam. 25:24) [20 ga Afrilu, w02 11/1 shafi na 4 sakin layi na 3 da shafi na 5 sakin layi na 4]

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba