Tsarin Ayyuka na Makon 9 ga Maris
MAKON 9 GA MARIS
Waƙa ta 44 da Addu’a
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl babi na 21 sakin layi na 9-15 (minti 30)
Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 1 Sama’ila 1-4 (minti 8)
Na 1: 1 Sama’ila 2:30-36 (minti 3 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Mene Ne Littafi Mai Tsarki Ya Annabta Game da Almasihu?—igw 10 (minti 5)
Na 3: Me Ya Sa Yesu Ne Shugaban Bangaskiyarmu da Mai Cikanta?—Ibran. 12:2 (minti 5)
Taron Hidima:
Jigon Wata: ‘Ku Zama Shiryayyu don Kowane Kyakkyawan Aiki.’—Tit. 3:1.
Waƙa ta 45
Minti 10: ‘Ku Zama Shiryayyu don Kowane Kyakkyawan Aiki.’ Jawabi a kan jigon wata. Ka Karanta kuma ka tattauna Misalai 21:5 da Titus 3:1 da kuma 1 Bitrus 3:15. Ka yi bayani a kan yadda yin shiri da kyau yake amfanar Kiristoci. Ka ɗan ambata wasu abubuwan da za a tattauna a Taron Hidima na wannan watan, kuma ka nuna yadda suke da nasaba da jigon watan.
Minti 10: Ka Gana da Mai Kula da Makarantar Hidima ta Allah. Mene ne aikinka ya ƙunsa? Ta yaya kake yin shiri don gudanar da makaranta a kowane mako? Me ya sa ya kamata ɗalibai su shirya jawabansu da kyau? Ta yaya dukan masu sauraro za su amfana idan suka shirya jawaban da za a yi a makaranta kafin su halarci taro?
Minti 10: “Kuna Yin Shiri don Ranar Tuna da Mutuwar Yesu?” Tattaunawa. Ka ɗan tattauna abin da ke shafi na 2 na Hidimarmu ta Mulki na Maris, 2013. Ka sa a yi gwajin da zai nuna wani mai shela yana marabtar baƙo da ya zo taron Tuna da Mutuwar Yesu.
Waƙa ta 8 da Addu’a