Tsarin Ayyuka na Makon 29 ga Disamba
MAKON 29 GA DISAMBA
Waƙa ta 37 da Addu’a
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl babi na 18 sakin layi na 1-8 (minti 30)
Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Joshua 12-15 (minti 10)
Bitar Makarantar Hidima ta Allah (minti 20)
Taron Hidima:
JIGON WATA: Ku fito da abubuwa “masu kyau” daga ajiya mai kyau da aka ba mu.—Mat. 12:35a.
Waƙa ta 89
Minti 20: Ku Ci Gaba da Koya wa Ɗalibanku da ’Ya’yanku Abubuwa “Masu Kyau.” (Mat. 12:35a) Tattaunawa. Ka bayyana abubuwan da ya wajaba ɗalibanmu da yaranmu su yi bisa ga nassosin da ke gaba: 1 Korintiyawa 13:11; 1 Bitrus 2:2, 3. Ka bayyana abin da ake nufi da “ɗanɗana” “madara” ta Kalmar Allah da kuma yadda za mu iya taimaka wa ɗalibanmu da yaranmu su yi hakan. Ka bayyana ƙa’idar da ke Markus 4:28. (Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Disamba, 2014, shafi na 12, sakin layi na 6-8.) Ka gana da wani mai shela da ya ƙware ko mahaifi ko kuma mahaifiya da za ta iya bayyana yadda ta taimaka wa ɗalibinta ko ɗanta ya samu ci gaba a ibadarsa ga Jehobah.—Afis. 4:13-15; ka duba Tambayoyin Masu Shela a Hidimarmu ta Mulki ta Mayu 2014.
Minti 10: “Ku Rarraba Abubuwa ‘Masu Kyau’ ta Wajen Karɓan Baƙi (Mat. 12:35a).” Tattaunawa. Ta yaya wasu suka amfana don sun kasance da halin karɓan baƙi? Ka ba masu sauraro dama su yi kalami a kan yadda za mu nuna halin karɓan baƙi ga ’yan’uwa, musamman waɗanda suke hidima ta cikakken lokaci. Ka ambata tsarin da ikilisiya ta kafa don ciyar da ɗan’uwan da ya zo yin jawabi.
Waƙa ta 124 da Addu’a