Tsarin Ayyuka na Makon 14 ga Yuli
MAKON 14 GA YULI
Waƙa ta 1 da Addu’a
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl babi na 10 sakin layi na 1-7 (minti 30)
Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Levitikus 21-24 (minti 10)
Na 1: Levitikus 23:1-14 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Abin da Ya Sa Yake da Muhimmanci Mu Yi Imani da Yesu Idan Muna Son Ceto—td 43B (minti 5)
Na 3: Waɗanda Suke Yin Mugun Abu Za Su Iya Canjawa Kuwa?—lr babi na 25 (minti 5)
Taron Hidima:
Waƙa ta 45
Minti 10: Ku Shirya don Kamfen na Musamman a Watan Agusta. Ka ba da kofi ɗaya na sabuwar warƙar nan A Ina Ne Za Mu Sami Amsoshin Muhimman Tambayoyi? ga duk wanda bai da shi. Ka sa a yi gwaji guda biyu bisa ga gabatarwa da ke shafi na 4. A gwaji na farko, ka sa a nuna yadda za a iya ba da warƙar ga mutane gaba ɗaya. Sa’an nan ka sa a nuna yadda za a iya ba da warƙar idan mutum yana son saƙonmu kuma yana so a tattauna da shi. Ka ƙarfafa dukan masu shela su yi wannan kamfen ɗin.
Minti 5: Ku Amfana Daga Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana. Tattaunawa. Ka ba masu sauraro dama su faɗi lokacin da suke karanta littafin nan Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana da kuma yadda hakan ya amfane su.
Minti 15: “Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Yin Wa’azi—Yadda Za Mu Soma Taɗi da Burin Yin Wa’azi.” Tattaunawa. Ka sa a yi gwaji.
Waƙa ta 107 da Addu’a