Sabon Bidiyo don Soma Nazari da Mutane
An saka wani gajeren bidiyo mai jigo Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki? a dandalin jw.org don mutane a faɗin duniya. An shirya wannan bidiyon ne don a motsa waɗanda suke son saƙonmu su amince a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su kyauta. Za a iya samun wannan bidiyon ta wajen danna inda aka rubuta “In Kana So A Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki da Kai,” a ƙarshen shafin farko na dandalinmu ko kuma ta wajen yin amfani da abin da ke farin akwatin da ke bayan sababbin warƙoƙinmu, wato fasahar QR code don a shiga dandalinmu. Za mu iya yin amfani da wannan bidiyon a hanyoyi masu kyau da aka nuna a gaba.
Idan kuka koma ku ziyarci wanda ya karɓi saƙonmu, ku gaya masa: “Zan so in nuna maka wani gajeren bidiyo da ya bayyana yadda za ka iya samun amsoshi ga tambayoyinka a cikin Littafi Mai Tsarki.” Idan ya yarda, sai ka nuna masa bidiyon a wayarka ko dai wata na’ura da kake da ita ko kuma a tasa na’urar.
Idan muka ba wani ɗaya daga cikin sababbin warƙoƙinmu sa’ad da muke wa’azi a inda akwai jama’a ko kuma a duk inda muka samu zarafi, zai dace mu nuna masa wannan fasahar kuma mu ƙarfafa shi ya bi kanta da na’urar da za ta iya yin hakan. Tun da yake wannan fasahar QR code za ta iya kai mutum nan take zuwa shafin da aka saka wannan bidiyon a harsuna da yawa a dandalinmu, za ka iya nuna wa mutumin bidiyon nan da nan da na’urarka.
Ka sanar da abokan aikinka da na makarantarka da kuma danginka game da bidiyon kuma ka gaya musu cewa za ka so ka nuna musu idan suna so, ko kuma ka aika musu adireshin da bidiyon yake a cikin dandalinmu don su kalli bidiyon da kansu.
Wannan sabon tanadin zai iya taimaka mana mu soma nazari da mutane da yawa, kuma ta hakan za mu taimaka wa masu tawali’u su ƙulla dangantaka da Allah.—Mat. 18:4.