Labarai
◼ Ostareliya: A dā can, wani wayayyen mutum mai suna John yana zuwan coci a lokacin da yake yaro. Amma, daga baya ya daina gaskata da Allah gaba ɗaya. Wani majagaba ya ba shi ƙasidar nan Was Life Created?, sa’an nan daga baya ya kawo masa ƙasidar nan The Origin of Life—Five Questions Worth Asking. Majagaban ya taimaka masa ya ci gaba da son saƙonmu ta wajen kai masa sababbin mujallu da kuma nuna masa duk wani talifin da ke tattauna batun halitta ko kuma annabcin Littafi Mai Tsarki. A lokacin da majagaban ya ga cewa John ya soma sha’awar Littafi Mai Tsarki, sai ya ba shi littafin nan The Bible—God’s Word or Man’s? Da John ya gama karanta littafin, sai ya soma cewa ya gaskata da wanzuwar Allah, amma bai yarda cewa za a iya saninsa ba. Hakan ya sa majagaban ya nuna masa littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? kuma suka yi nazarin sakin layi na 8 a shafi na 20 da sakin layi na 13-16 a shafuffuka na 23-24. Nassosin da aka rubuta a wurin sun burge John sosai har ya ce: “Ina ganin zai dace in sake karanta Littafi Mai Tsarki.”
◼ Meziko: Wani mutum ya gaya ma wani ɗan’uwa cewa bai yarda wai Allah ne ya hure Littafi Mai Tsarki ba. Ɗan’uwan ya tambaye shi ko zai yarda ya ba shi dama don ya nuna masa tabbaci cewa Allah ne ya hure Littafi Mai Tsarki. Bayan sun tattauna sau da sau, sai abubuwan da mutumin yake koya suka fara taɓa zuciyarsa, musamman ma batun ɗabi’a. Sai mutumin ya gaya wa ɗan’uwan cewa: “A lokacin da muka soma karanta Littafi Mai Tsarki tare, ban ga bambancin shawarwarin da ke cikinsa da wasu littattafai ba, saboda haka ban ko damu da abin da nake karantawa ba. Amma yanzu, a duk lokacin da muka karanta shi, musamman ma idan muka taɓa batun ɗabi’a, zuciyata tana damuna sosai.”
◼ Amirka: Sa’ad da wasu ma’aurata suke wa’azi na musamman a manyan birane, sun haɗu da wata mata daga ƙasar Taiwan da ta ce ta yarda cewa akwai Allah, amma tana ganin an rubuta Littafi Mai Tsarki domin Turawa ne kawai. Ta je wurin teburin da suke ajiye littattafai domin ta rasa inda ta dosa a rayuwa ko da yake ita ’yar gata ce. Tana sa rai cewa Littafi Mai Tsarki zai iya taimakon ta ta yi rayuwa mai ma’ana. Ma’auratan suka soma nazari da ita daga littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa, tare da ƙasidar nan Lasting Peace and Happiness—How to Find Them. Maimakon su tattauna babi na 2 a cikin littafin, sai suka tattauna wani sashe a ƙasidar da ya ce “A Guidebook for the Blessing of All Mankind.” Bayan suka gama nazarin sakin layi na ɗaya zuwa na shida a sashen, matar ta yi mamakin yadda Littafi Mai Tsarki ya sha gaban dukan littattafan addinai. Da suka tattauna annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki da suka cika, sai ta ce: “Ban ga wani littafi da ke ɗauke da bayanai da suka yi daidai kamar Littafi Mai Tsarki ba!”
◼ Jafan: Wani maigida ya gaya ma wani mai shela cewa bai gaskata da wanzuwar Allah ba, amma mai shelar ya ci gaba da ziyartarsa, kuma ya riƙa nuna masa talifofin nan “Was It Designed?” a cikin mujallun Awake! A hankali, mutumin ya soma yarda cewa akwai Mahalicci. Yanzu ya gaskata cewa akwai Allah kuma mai shelar yana nazari daga shi da ƙasidar nan Albishiri Daga Allah!
◼ Kyanada: Wata ’yar’uwa ta ba wata mata mujallunmu a lokacin da matar za ta je shigar motarta. A lokacin da ’yar’uwarmu ta dawo, matar ta ƙi da saƙonmu kuma ta ce ba ta yi imani da Allah ba. ’Yar’uwarmu ba ta fid da rai a kanta ba, amma ta ƙudura cewa sai ta ba ta ƙasidar nan A Satisfying Life—How to Attain It. A lokacin da ta sami matar a gida, sai ta gaya mata cewa ko da yake ta san matar ba ta gaskata da Allah ba, ta yi ta tunanin ta domin ta san cewa matar mahaifiya ce kuma mijinta ba ya tare da ita. ’Yar’uwar ta nuna mata sakin layi na 6 a shafi na 4 a cikin ƙasidar, inda aka nuna kasawar shawarar ’yan Adam. Sai ta gaya mata ta karanta shawarwari a kan renon yara a cikin darasi na 2. Matar ta yi farin cikin samun wannan ƙasidar.