Bitar Makarantar Hidima ta Allah
Za a tattauna tambayoyin da ke gaba a Makarantar Hidima ta Allah a makon 28 ga Oktoba, 2013.
1. Mene ne Littafi Mai Tsarki yake nufi sa’ad da ya ce mu ci gaba da sanin “nufin Kristi”? (1 Kor. 2:16) [2 ga Satumba, w08 7/15 shafi na 27 sakin layi na 7]
2. A waɗanne hanyoyi ne za mu “guje ma fasikanci”? (1 Kor. 6:18) [2 ga Satumba, w08 7/15 shafi na 27 sakin layi na 9; w04 3/1 shafi na 10 sakin layi na 9]
3. Mene ne Bulus yake nufi sa’ad da ya rubuta cewa: ‘Bari mata su yi shuru cikin ikilisiyoyi?’ (1 Kor. 14:34) [9 ga Satumba, w12 10/1 shafi na 9, akwati]
4. Mene ne Kiristoci dattawa za su iya koya daga kalmomin Bulus da aka rubuta a 2 Korintiyawa 1:24? [16 ga Satumba, w13 1/15 shafi na 27 sakin layi na 2-3]
5. Ta yaya za mu bi ja-gorar da ke 2 Korintiyawa 9:7? [23 ga Satumba, w09 2/15 shafi na 13 sakin layi na 17]
6. Ta yaya za mu amfana daga bin shawara da Bulus ya bayar a Galatiyawa 6:4? [30 ga Satumba, w12 12/15 shafi na 13 sakin layi na 18]
7. Mene ne “kiyaye ɗayantuwar ruhu cikin ɗaurin salama” yake nufi? (Afis. 4:3) [7 ga Oktoba, w12 7/15 shafi na 28 sakin layi na 7]
8. Yaya Bulus ya ji game da sadaukarwar da ya yi? (Filib. 3:8) [14 ga Oktoba, w12 3/15 shafi na 27 sakin layi na 12]
9. Mene ne muhimmancin gargaɗin nan: “Kada fa mu yi barci, kamar sauran mutane”? (1 Tas. 5:6) [21 ga Oktoba, w12 3/15 shafi na 10 sakin layi na 4]
10. Ta yaya mutuwar Yesu ta zama “daidaitacciyar fansa”? (1 Tim. 2:6, NW) [28 ga Oktoba, w11 6/15 shafi na 13 sakin layi na 11]