Tsarin Ayyuka na Makon 23 ga Satumba
MAKON 23 GA SATUMBA
Waƙa ta 109 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
wt babi na 15, sakin layi na 1-9 (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 2 Korintiyawa 8-13 (minti 10)
Na 1: 2 Korintiyawa 10:1-18 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Zancen Cetar da Rai Ba Hujjar Taka Dokar Allah Ba Ne—td 24B (minti 5)
Na 3: Mene Ne Ma’anar Abin da Aka Rubuta a Littafin 1 Korintiyawa 10:13? (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 43
Minti 5: “Zan Karɓi Littattafanku Idan Kuka Karɓi Nawa.” Tattaunawa. Ka ba masu sauraro dama su faɗi yadda suka taɓa bi da irin wannan yanayin.
Minti 10: Mene Ne Muka Cim Ma a Bara? Jawabin da mai kula da hidima zai ba da. Ka yi bitar rahoton wa’azi da ikilisiya ta yi a shekarar hidima da ta gabata, ka mai da hankali ga abubuwa masu kyau da aka cim ma, kuma ka yaba wa ’yan’uwa a inda ya kamata. Ka ambata fanni ɗaya ko biyu na yin wa’azi da ’yan’uwa suke bukatar daɗa ƙoƙari a kai a shekara mai zuwa, kuma ka ba da shawarwari masu kyau da za su iya taimaka musu su yi hakan.
Minti 15: Mene Ne Muka Koya? Tattaunawa. Ka sa a karanta Ayyukan Manzanni 16:19-40. Ka tattauna yadda wannan labarin zai iya taimaka mana sa’ad da muke yin wa’azi.
Waƙa ta 44 da Addu’a