Tsarin Ayyuka na Makon 16 ga Satumba
MAKON 16 GA SATUMBA
Waƙa ta 21 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
wt babi na 14, sakin layi na 10-15 da akwati (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 2 Korintiyawa 1-7 (minti 10)
Na 1: 2 Korintiyawa 1:15–2:11 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Karɓan Jini a Asibiti Ya Saɓa wa Dokar Allah—td 24A (minti 5)
Na 3: Mene Ne Ya Dace Mutum Ya Yi don Ya Samu Mafaka Cikin Sunan Jehobah?—Zaf. 3:12 (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 41
Minti 10: Matasa—Me Za Ku Yi da Rayuwarku?—Sashe na 2. Jawabi bisa ga bayanin da ke cikin warƙar nan Matasa—Me Za Ku Yi da Rayuwarku?, daga sakin layi na 10 zuwa sakin layi na ƙarshe. Ka ɗan gana da wani da ya soma hidima ta cikakken lokaci tun yana matashi. Me ya motsa shi ya tsai da shawarar yin hidima ta cikakken lokaci? Waɗanne albarka ne ya samu?
Minti 10: Idan Ka Fita Wa’azi Kai Kaɗai. Tattaunawa. (1) Me zai taimaka maka ka yi farin ciki idan kai kaɗai ne ka fita wa’azi? (2) Idan ka je ka ziyarci ɗalibinka kai kaɗai, waɗanne matakai ne ya kamata ka ɗauka don ka yi hattara? (3) Idan ranar da muke son mu fita wa’azi ba ranar da ikilisiyarmu ta ayyana don fita wa’azi ba ne, ta yaya za mu ƙarfafa wasu a cikin ikilisiyar su fita tare da mu a ranar? (4) Waɗanne sakamako masu kyau ne mukan samu idan muka fita wa’azi mu kaɗai a wasu lokatai idan yin hakan ba zai kasance da haɗari ba?
Minti 10: “Su Wane Ne Suke Yin Nufin Jehobah a Yau?” Tambayoyi ana ba da amsoshi. Ka ɗan yi bitar tsarin ƙasidar nan da kuma abubuwan da ke cikinta.—Ka duba Hidimarmu ta Mulki na Maris 2013, shafi na 3.
Waƙa ta 107 da Addu’a