Tsarin Ayyuka na Makon 8 ga Yuli
MAKON 8 GA YULI
Waƙa ta 43 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
wt babi na 9, sakin layi na 11-18, da akwati (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Ayyukan Manzanni 15-17 (minti 10)
Na 1: Ayyukan Manzanni 16:16-34 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Me Zai Taimaka wa Kirista Ya Yi Farin Ciki Sa’ad da Ake Tsananta Masa?—Mat. 5:11, 12 (minti 5)
Na 3: Allah Ya Haramta Bautar Kakanni—td 10A (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 75
Minti 10: Hanyoyin Yin Wa’azin Bishara—Ku Ja-goranci Masu Son Gaskiya Zuwa Ƙungiyar Jehobah. Jawabi bisa ga bayanin da ke littafin nan Organized to Do Jehovah’s Will, shafi na 99, sakin layi na 2, zuwa shafi na 100, sakin layi na 1. Ka ba masu sauraro dama su faɗi yadda suka yi amfani da ƙasidar nan, Su Wane Ne Suke Yin Nufin Jehobah A Yau? wajen yi wa ɗalibansu ja-gora zuwa ƙungiyar Jehobah.
Minti 10: Ku Gwada Jehobah Kuma Za Ku Sami Albarka Mai Yawan Gaske. (Mal. 3:10) Ka gana da majagaba na kullum guda biyu ko uku. Mene ne suka fi jin daɗinsa a aikin majagaba? Ta yaya hidimar majagaba ta taimaka musu su kusaci Jehobah sosai? Ka gaya musu su faɗi abubuwa masu daɗin ji da suka faru sa’ad da suke wa’azi. Ka kammala ta wajen ƙarfafa masu shela su yi shawara ko za su iya daidaita harkokinsu don su soma hidimar majagaba na kullum a watan Satumba.
Minti 10: “Ku Bi Gurbin Annabawa—Joel.” Tambayoyi ana ba da amsoshi.
Waƙa ta 54 da Addu’a