Bitar Makarantar Hidima ta Allah
Za a amsa waɗannan tambayoyi na gaba a Makarantar Hidima ta Allah a makon 25 ga Fabrairu, 2013. An saka kwanan watan da za a tattauna waɗannan bayanan domin ku yi bincike sa’ad da kuke shirya makaranta a kowane mako.
1. Me ya sa Yesu ya ce waɗanda “su ke da ɓacin zuciya” za su yi farin ciki? (Mat. 5:4) [7 ga Janairu, w09 2/15 shafi na 6 sakin layi na 6]
2. A cikin addu’ar da Yesu ya koya wa almajiransa, mene ne yake nufi sa’ad da ya ce: “Kada ka kai mu cikin jaraba”? (Mat. 6:13) [7 ga Janairu, w04 2/1 shafi na 22 sakin layi na 13]
3. Me ya sa Yesu ya ce almajiransa ba za su ƙarasa aikin wa’azi ba kafin ‘Ɗan mutum ya dawo?’ (Mat. 10:23) [14 ga Janairu, w10 9/15 shafi na 10 sakin layi na 12]
4. Waɗanne abubuwa biyu ne kwatanci na ƙwayar mastad ya koya mana? (Mat. 13:31, 32) [21 ga Janairu, w08 7/15 shafuffuka na 17-18 sakin layi na 3-8]
5. Mene ne ya kamata mu yi sa’ad da muka ga cewa laifin da aka yi mana yana da wuyar gafartawa? (Mat. 18:15-17) [28 ga Janairu, w11 8/15 shafi na 28 sakin layi na 6]
6. A kan menene Yahuda ya yi nadama? (Mat. 27:3-5) [11 ga Fabrairu, w08 1/15 shafi na 31 sakin layi na 3]
7. Me ya sa aka kira Yesu “Ubangiji ne har na ran assabbaci”? (Mar. 2:28) [18 ga Fabrairu, w08 2/15 shafi na 28 sakin layi na 7]
8. Me ya sa Yesu ya amsa yadda ya yi game da mahaifiyarsa da ’yan’uwansa, kuma mene ne wannan yake koya mana? (Mar. 3:31-35) [18 ga Fabrairu, w08 2/15 shafi na 29 sakin layi na 2]
9. A Markus 8:22-25, me ya sa Yesu ya warƙar da wani makaho a hankali, kuma me za mu koya daga wannan? [25 ga Fabrairu, w00 3/1 shafi na 10 sakin layi na 7]
10. Mene ne muka koya daga yadda Yesu ya yi sa’ad da Bitrus ya tsauta masa a Markus 8:32-34? [25 ga Fabrairu, w08 2/15 shafi na 29 sakin layi na 3]