Tsarin Ayyuka na Makon 20 ga Agusta
MAKON 20 GA AGUSTA
Waƙa ta 83 da addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki Na Ikilisiya:
cl shafuffuka na 226 zuwa 228, da akwati (minti 25)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Ezekiyel 32-34 (minti 10)
Na 1: Ezekiyel 34:15-28 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Dalilin da Ya Sa Ake Tsananta wa Kiristoci na Gaske—td 21A (minti 5)
Na 3: Dalilin da Ya sa Addu’a Mai Ma’ana Ba Ta Kalami Ba Ne Kawai—Zab. 145:18; Mat. 22:37 (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 76
Minti 5: Sanarwa.
Minti 10: Ka gana da ɗan’uwa guda ko biyu da suke hidima ta cikakken lokaci. Me ya sa suka shiga hidima ta cikakken lokaci? Waɗanne ƙalubale ne suka fuskanta, amma me ya taimaka musu su ci gaba da hidimar? Kuma ta yaya Allah ya albarkace su? Ka ƙarfafa ’yan’uwa su yi hidimar majagaba idan da hali a shekarar hidimar da ke tafe.
Minti 20: “Kun Yi Shiri don Aukuwar Bala’i?” Tambayoyi ana amsawa. Ka haɗa da kalaman da ke Hasumiyar Tsaro ta Janairu-Maris 2012, shafuffuka na 6, 7.
Waƙa ta 70 da Addu’a