Tsarin Ayyuka na Makon 13 ga Agusta
MAKON 13 GA AGUSTA
Waƙa ta 63 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl shafi na 221 zuwa shafi na 226 (minti 25)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Ezekiyel 28-31 (minti 10)
Na 1: Ezekiyel 28:17-26 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Ka Ware Ƙage Daga Gaskiya Game da Yesu Kristi (minti 5)
Na 3: Ingantawa Don Hidimar—td 31B (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 115
Minti 5: Sanarwa.
Minti 10: Ku Sa Maigidan Ya Kasance a Shirye don Ziyararku ta Gaba. Ku tattauna waɗannan tambayoyi: (1) Me ya sa yake da kyau mu sa maigida ya kasance a shirye don ziyararmu ta gaba, kuma ta yaya za mu yi hakan? (2) Ta yaya za mu zaɓi tambaya mai daɗi wadda maigidan zai so ya amsa a ziyararmu ta gaba? (3) Me ya sa yake da kyau ku sa ranar da za ku sake komawa ku tattauna, kuma idan zai yiwu ku karɓi adireshinsa da lambar wayarsa? (4) Me ya sa ya dace mu koma da wuri don mu ziyarci mutumin, mai yiwuwa bayan ’yan kwanaki? (5) Mene ne ya kamata mu rubuta bayan mun yi wa wani wa’azi da farko?
Minti 20: “Taron Gunduma da Muke Yi Suna Ba da Shaida Mai Kyau Game da Gaskiya.” Tambayoyi ana amsawa. Ka tattauna “Tunasarwa Game da Taron Gunduma na Shekara ta 2012.” Sa’ad da kake tattauna sakin layi na 9, ka gayyaci mai kula da hidima ya zo ya bayyana shirin da ikilisiyar ta yi na rarraba takardar gayyata.
Waƙa ta 119 da Addu’a