Rahotannin Wa’azi
Idan aka kwatanta da avirejin watan Disamba ta 2010, an samu ƙarin masu shela 13,627, shi ya sa masu shela 308,436 ne suka ba da rahoton hidimar fage a watan Disamba ta 2011. Waɗannan masu shela sun yi amfani da awoyi 5,084,977 suna wa’azi. Hakan yana da kyau, domin yawancin ikilisiyoyi sun halarci taron gunduma a wannan watan.