Sanarwa
◼ Littafin da za a ba da a watan Yuni: Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Ka ƙoƙarta ka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da su a haɗuwarku ta farko. Idan masu gida suna da littafin amma ba su yarda a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su ba, masu shela suna iya ba da tsohuwar mujalla ko kuma ƙasidar da ta tattauna abin da mai-gidan ke sha’awa. Yuli da Agusta: Ku yi amfani da ɗaya cikin ƙasidun nan masu shafuffuka 32: Ka Saurari Allah ko kuma Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada, Za Ka Iya Zama Abokin Allah! kuma ku yi ƙoƙari don ku soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutanen. Sa’ad da kuke koma ziyara, ku ba da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ko kuma ku ba da wata ƙasidar da jigon ya yi daidai da abin da mutumin yake so. Satumba: Hasumiyar Tsaro da Awake! Sa’ad da kake koma ziyara, ka gabatar da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ko kuma idan suka dace da bukatun mutumin, ka ba shi ɗaya daga cikin ƙasidun nan Ka Saurari Allah ko kuma Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada, kuma ka ƙoƙarta ka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da shi.
◼ Ana ƙarfafa kowa ya kalli bidiyon nan Our Whole Association of Brothers. Idan kuna bukatar bidiyon, za ku iya rubuta yawan waɗanda za a aika wa ikilisiyarku.
◼ Muna so mu sanar da ku cewa mun daina amfani da tsohon adireshin Ofishin Bethel da ke Legas. Sabon lambar akwatin gidan waya na Ofishin Bethel da ke Legas shi ne: P.M.B. 21845, Alausa 100212, Ikeja, Lagos State.