Tsarin Ayyuka na Makon 4 ga Yuni
MAKON 4 GA YUNI
Waƙa ta 103 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki Na Ikilisiya:
cl shafuffuka na 189 zuwa 192 (minti 25)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Irmiya 51-52 (minti 10)
Na 1: Irmiya 52:17-27 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Tilas ne Kiristoci Su Yi Biyayya da Ƙa’idar Kan-Gida—td 7B (minti 5)
Na 3: A Wacce Hanya Ce ’Yan Adam Za Su Iya Kasance a “Maɓuyan” Jehobah?—Zab. 91:1, 2, 9 (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 57
Minti 5: Sanarwa.
Minti 10: Yadda Za Mu Motsa Zukatan Mutane—Sashe na 2. Jawabin da aka ɗauko daga littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education, shafi na 261, sakin layi na 2, zuwa ƙarshen shafi na 262.
Minti 10: Bukatun ikilisiya.
Minti 10: Hanyoyin Ba da Mujallu a Watan Yuni. Tattaunawa. Ka yi amfani da minti ɗaya ko biyu don ka ambata wasu cikin talifofin da mutane a yankinku za su so. Bayan haka, ka ba ’yan’uwa dama su faɗi tambayar da za su yi wadda za ta sa masu gida su yi sha’awar batun da suke gabatarwa da kuma nassin da za su karanta wanda ya yi daidai da kan maganar da ke bangon Hasumiyar Tsaron. Ka yi hakan ma da talifofin da jigon Awake! ya tattauna kuma idan da lokaci ka zaɓi wani talifi dabam a cikin mujallun don ka tattauna shi. Ka sa a gwada yadda za a ba da kowannen su.
Waƙa ta 61 da Addu’a